1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Gwamnati ta tsaurara tsaro a Bamenda

Zulaiha Abubakar MAB
September 11, 2018

Sakamakon hare-haren da 'yan aware su ka kai kan motocin haya dauke da fasinjoji da zummar toshe hanyoyin da ke shiga yankin masu magana da harshen Ingilishi, gwamnatin Kamaru ta kara yawan sojoji a yankin Bamenda.

https://p.dw.com/p/34fta
Kamerun Sprachenstreit Englisch
Hoto: Getty Images/AFP

Wasu mazauna garin Akum da ke da nisan kilomita 10 da Bamenda sun koma bakin aiki bayan irin hare-haren da mayakan 'yan awaren kasar ta Kamaru suka kai wa motocin haya makare da fasinjoji tare da katse hanyoyin sadarwar kasar.

Aleh solomon Injiniyan sadarwa da ya gane wa idanunsa abin da ya faru ya ce "lokacin da muka zo da safe don gudanar da gwaji, mun ga an datse wayar sadarwa mai tsawon kilomita 15 da rabi zuwa Bamenda, matsalar ta shafi dukkanin kafafen sadarwar da ke wannan yanki, kowa ma ta shafeshi."

Baya ga hare-haren da 'yan awaren suka saba kaiwa, a halin yanzu sun bullo da wata sabuwar hanyar yin gaba da kayan aikin hanya ko kuma banka wuta a kan kayayyakin da gwamnati ta jibge don aikin raya kasa.   

Tshirt Francophonization
Anglophone sun zargi sauran 'yan kamaru da mayar da su saniyar wareHoto: Moki Kindzeka

Thomas Akwon shugaban wani kamfanin aikin hanyoyi ya ce "ma'aikatana sun shaida min cewar wasu mutane dauke da bindigogi sun zo sun kuma umarce su da shiga cikin wata mota a gefen hanya, suna ji suna gani mutanen suka yi gaba  da injinan da motar da muke aiki da ita ."

Duk da matakan dakile wannan rikici da gwamnatin Kamaru ta dauka, mayakan 'yan awaren sun aike wa kanfanin sufurin motocin haya ta Amour Mezam wata budaddiyar wasika dauke da gargadi kan ta guji bai wa rudunar tsaro goyon baya, inji Jules Ngouls jami'in hukumar inda ya ce "sun ce Amour Mezam ne kamfanin da ke jigilar 'yan sanda da kuma sauran jami'an tsaro zuwa Bamenda domin yaki da su."

Kamerun Sprachenstreit um Englisch
'Yan aware na nasarar kashe jami'an tsaro a yankin IngilishiHoto: Getty Images/AFP

 'Yan awaren sun dauki alhakin hare-haren da suka faru a karshen makon da ya gabata tare da jaddada aniyarsu ta hana gudanar da zabe a yankin da ake magana da Ingilishi a Kamaru. Suka ce bbua gudu babu ja da baya, har sai sun ga tabbatuwar kasar Ambazoniya kafin su shirya zabensu.

Gwamnati ta Kamaru ta kara daukan tsauraran matakai don tsare Bamenda da sauran kauyukan da ke makwabtaka da yankin.