1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: An kashe sojojin gwamnati

Abdul-raheem Hassan
December 19, 2017

Sojoji hudu sun mutu a wani sabon artabu da ya barke tsakanin 'yan aware da sojojin gwamnati a garin Mafa da ke Kudu maso yammacin kasar Kamaru.

https://p.dw.com/p/2pbrc
Symbolbild zur Nachricht - Streitkräfte in Kamerun zerschlagen Boko-Haram-Schule
Hoto: Getty Images/Afp/Reinnier Kaze

Hukumomin gwamnati a Kamaru sun ce dakarun gwamnatin sun kashe wasu daga cikin 'yan awaren kasar bayan da sabon rikin ya barke, sai dai basu bayyana adadin wadanda aka kashe ba kawo yanzu.

Shugaban 'yan awaren da ke son kafa yankin Ambazoniya John Fru Ndi, ya caccaki gwamnati na rashin daukar matakan da suka dace a duk lokacin da aka samu kunnowar rikicin a yankin.

Jami'an tsaro sun kashe mutane da dama tun bayan da aka fara zanga-zangar neman kafa yanki mai cin gashin kai a Kamaru, hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai 'yan yankin 40,000 da ke gudun hijira a makwabciyar kasar Najeriya.