Kamala Harris: Macen da ta yi fice wajen shiga sahun farko a komai na rayuwa
Kamala Harris, Bakar fata mai tushe da Kudancin Asiya, bakar fata ta farko da ta zama mataimakiyar shugaban Amurka. Ta tsallake kalubale kafin cimma nasarar rayuwa—ko za ta zama mace farko da za ta shugabanci Amurka?
Iyalan 'yan gudun hijira
An haifi Kamala Devi Harris a Oakland da ke California a ranar 20 ga watan Oktoban 1964. Mahaifinta mai suna Donald J. Harris, fitaccen masanin kimiyya ne 'dan asalin Jamaica. Mahaifiyarta mai suna Shyamala Gopalan Harris, 'yar asalin kasar India, kwararriya ce a fannin kimiyya, inda ta yi fice wajen bincike kan cutar sankarar mama.
Ta ba mu tarbiyyar zama jajirtattun bakaken fata
Bayan mutuwar auren iyayensu, Kamala Harris (daga hagu) tare da kanwarta Maya sun zauna da mahaifiyarsu a Montreal a Kanada tana da shekaru 12. Gopalan Harris ta mutu a shekarar 2009 sakamakon ciwon kansa. "Ta ba mu tarbiyyar zama jajirtattun bakaken fata, ta sa mana kishin asalinmu Indiya,'' in ji Harris lokacin da ta karbi matsayin takarar mataimakiyar shugaban kasa a jam'iyyar Democrats a 2020.
'Yar gwagwarmayar kare hakkin al'umma
Kamala da mahaifanta sun yi fice wajen fafutukar kare hakkin al'umma a Amurka, kuma ta ce wannan ya yi tasiri wajen gina rayuwarta, kamar yadda ta fada a littafin tarihinta. An yi mata wannan hoto a watan Nuwamban shekarar 1982, tana da shekaru 18, a jami'ar Howard a Washington, lokacin zanga-zangar kin jinin mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu.
Tsangayar aikin koyon harkokin shari'a a California
Harris ta kammala jami'ar Howard University a shekarar 1986 sannan ta tafi kwalejin nazarin shari'a ta Hastings da ke jami'ar California a San Francisco. Ta fara aiki ne a shekarar 1990, a matsayin lauya a gundumar Alameda da ke California.
Mace ta farko da ta rike matsayin babbar lauyar San Francisco
Yayin da Kamala ke karbar rantsuwar kama aiki a 2004, a matsayin mace ta farko da ta rike matsayin babbar lauyar San Francisco, kuma mace bakar fata ta farko da ta rike mukamin, a daidai lokacin da mahaifiyarta (daga tsakiya) ke rike da kundin dokokin hakkin bil'adama na Amurka. Kundin na kunshe da sadarori 10 na farkon kundin tsarin mulkin Amurka kan batun kare 'yancin 'dan adam da walwalwa.
Daga babbar mai shari'a ta gunduma zuwa kololuwa
A cikin watan Janairun 2011, Harris ta karbi matsayin babbar mai shari'a ta California—kuma mace ta farko, sannan kuma bakar fata mace ta farko da ta samu wannan matsayi.Ta fuskanci suka sosai kan adawarta da dokar kisa.
Tsunduma cikin fagen siyasa
A shekarar 2016, Harris ta yanke shawarar tsayawa takarar sanata a jihar California—kuma ta lashe zabe. Ta ajiye mukaminta na babbar mai shari'a sannan mataimakiin shugaban Amurka mai barin gado na lokacin Joe Biden ya rantsar da ita, a Janairun 2017. Mai gidanta Douglas Emhoff yana kusa da ita, wanda lauya ne, kuma sun yi aure a 2014.
Wani sabon mataki na tarihi
A ranar 20 ga Janairun 2021, aka rantsar da Kamala a matsayin mace ta farko a mukamin mataimakiiyar shugaban Amurka, kuma bakar fata ta farko da ta samu mukamin, inda aka karfafa matakan tsaro a zauren majalisar. A ranar 6 ga Janairun ne magoya bayan Donald Trump suka kutsa kai cikin ginin majalisar na Capitol, suna ikirarin cewa shi ne ya ci zaben shugaban kasa.
An dora mata alhakin magance kwararar bakin haure
Daya daga cikin ayyukan da shugaba Biden ya dora wa Harris shi ne yin duba na tsanaki kan matsalar kwararar bakin haure, musamman ma daga Kudancin Amurka. Ta kai ziyara wasu kasashen, ciki har da Guatemala a cikin watan Yunin shekarar 2021, domin lalubo bakin zaren matsalar. jam'iyyar Republican ta sha sukarta bisa zargin gaza katabus wajen magance wannan matsala.
Wace dama Harris k da ita zaben 2024?
Idan har Democrats ta zabi Harris a matsayin 'yar takarar shugaban kasa a hukumance a cikin watan Agusta, tana da kwanaki 100 na zabar mataimakinta don fafatawa da Donald Trump a yakin neman zabe. Tuni aka tara mata miliyoyin daloli tun ranar Lahadin da ta gabata, kuma masharhanta sun ce za ta iya janyo hankalin bakaken fata su zabe ta. Ko da yake batun launin fata ka iya zama mata cikias a zaben.
This gallery was originally written in German.