Kama bakar fatar Amirka bayan wariyar jinsi | Labarai | DW | 05.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kama bakar fatar Amirka bayan wariyar jinsi

Wasu matasa hudu bakar fata na hannun 'yan sandan Chicago na Amirka bisa zarginsu da aka yi da cin zarafin wani farar fata a wani bidiyon da suka saka a facebook.

Rundunar 'yan sandan birnin Chicago na Amirka ta sanar da kama wasu matasa hudu bayan wallafa wani bidiyo a shafin intanet da ke nuna yadda suka azabtar da wani farar fata bayan da suka daureshi. Dukkanin wadanda ke tsaren bakar fata ne, maza biyu da mata biyu, kuma ana zarginsu da nuna wariyar ga wani jinsi daban.

Wannan bidiyo da ya bazu a kafar sada zumunci na facebook ya nuna yadda matasan ke dariysa tare da furta kalaman kiyeyya ga farar fata da kuma zababben shugaban Amirka Donald Trump. Masu gudanar da bincike a jihar Illinois na Amirka sun bayyana cewar farar fatan ya kasa bayyana halin da ya samu kansa a ciki sakamakon dimaucewa da ya yi.

Shi  farar fatan an ganoshi ne a kan titunan birnin Chicago bayan da matasan da suka tsareshi na tsawo sa'o'i 48 suka ci zarafinsa.