Kalubalen tsaro sakamakon bullar kungiyar da ke da’awar aiki da Kur′ani kadai | Siyasa | DW | 16.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kalubalen tsaro sakamakon bullar kungiyar da ke da’awar aiki da Kur'ani kadai

Masarautar Kagara da ke jihar Naija a Najeriya ta koka game da take taken wasu mabiya addinin Musulunci da ke da’awar kin anfani da Haditsan Annabi.

Yanzu haka dai jami'an tsaro na saka ido akan take taken wani malamin addinin islama dake wa'azi tare da kira ga mabiyansa su daina anfani da haditsan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wwasallam, kamar yadda yake a karkashin shari'ar Musulunci. Shi dai wannan malami mai suna malam Abdullahi Sawaba, yana wa'azin cewar babu inda Kur'ani ya umarci Musulmi yayi anfani da haditsai, don haka haramun ne yin hakan.

Kuma kamar yadda sakataren masarautar Kagara, kuma Uban Doman Kagara, Alhaji Abdulkadir Bala Kagara, ya shaida wa wakilinmu Babangida Jibril ta wayar tarho, an kira malamai da suka yi da mukabala tare dashi, amma kuma ya dage akan akidar tasa:

Ya ce "Mun gayyacesu, kuma suka ce sun tsaya a wannan mataki, bisa abubuwan da suka karanta a Al-Kur'ani, kuma mun sanar da jami'an tsaro domin dasu a ka gudanar da wannan taro, bayan nan kuma mun umarci masu da'awa da su shiga kauyuka domin ilmantar da jama'a a kan gaskiyar lamarin.

To ko yaya akidar wannan malami take a karkashin tsarin addinin islama? Wannan itace tambayar da wakilinmu Babangida Jibril ya yi wa malam Musa Sulaiman, wani masanin addinin Islama:

"Matsalar tsaro wanda ya shafi addinin dai abu ne da ke ci gaba da hana ruwa gudu a harkokin Najeriya, lamarin da kuma a ke danganta wa da sakaci na jami'an tsaro. Zargin kuma da suka sha musantawa."

Dakile kalubalen tsaro a Najeriya

A wannan mako ne dai rundunar 'yan sanda a kasar, ta ce ta kafa wata runduna ta musanman ta masu kwance wa, da la'la'ta bama-bamai, domin dakile ayyukan 'yan ta'adda, masu saka bama-bamai a gurare daban-daban na kasar, matakin da kuma wasu 'yan kasar ke dauka an makaro.

To ko wace shawara malaman na addini ke da ita ga mabiya wannan akida? Har ila yau ga malam Musa Sulaiman:

"Shekarun baya dai gwamnatin jihar Naija ta dauki matakai na tarwatsa wani sansani na mabiya addinin Islama a wani gari da a ke kira Darul-Islam. Lamarin da kuma ya ja wo kace nace a ciki da wajen kasar. Kuma yanzu haka, gwamnati na fama da maharan 'yan kungiyar Boko Haram a wasu yankuna na Arewacin Najeriya."

Sai dai kuma kokarin da na yi domin jin ta bakin jami'an tsaro a jihar Naija da kuma mabiya ko shi kanshi malam Abdullahi Sawaba ko kuma kwamishinan addini na jihar Naija, game da wannan akida ya ci tura.

Mawallafi : Babangida Jibril

Edita : Saleh Umar Saleh

Sauti da bidiyo akan labarin