1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen jam'iyya mai mulki a zaben Mozambik

Yusuf BalaOctober 15, 2014

Jam'iyyar Frelimo mai mulki na fiskantar babban kalubale daga babbar jam'iyyar adawa ta Renamo da ma karamar jam'iyyar adawa ta MDM a zaben kasa baki daya.

https://p.dw.com/p/1DWBz
Wahlen Mosambik 15.10.2014 Filipe Nyusi
Hoto: Reuters/Grant Lee Neuenburg

Fiye da mutane miliyan 10 ne suka cancanci kada kuri'a dan zaben shugaban kasa da 'yan majalisar kasa da 'yan majalisar lardina.

An dai samu dogwayen layika a wasu tashoshin kada kuri'a wani abu da ke nuni da cewa mutanen da aka tsammaci zasu fito kada za su ninka kashi 44 daga cikin dari na adadin da aka samu a shekarar 2009.

Al'amuran zabe daga lokaci zuwa lokaci kan zama babban kalubale ga jam'iyya me mulki a ta Frelimo, tun lokacin da kasar ta samu 'yanci daga kasar Portugal a shekarar 1975 musamman daga bangaren babbar jam'iyyar adawa ta Renamo me ra'ayin adawa da gurguzu wacce a baya fafutukar ta ya kai kasar ga shiga yakin basasar shekaru goma sha shida.

Ko yaya masu sanya idanu daga kungiyar tarayyar turai ta EU suka ga yadda jama'a suka fito tashoshin kada kuri'ar? Judith Sargentini ita ke jan ragamar wannan tawaga da ke sanya idanu a zaben na Muzambik.

Wahlen Mosambik Filipe Nyusi und Armando Guebuza
Dan takaran Frelimo Filipe Nyusi da shugaba Armando GuebuzaHoto: Getty Images/AFP/ Gianluigi Guercia

"Mafi yawa tashoshin kada kuri'ar an bude su akan lokaci akwai kayan aiki da aka tanada akwai kuma mutane se dai ba lallai wadanda ke wakiltar jamiyyun da suka shiga takara ba".

A lokuta da dama a zabukan wannan kasa akan samu tashin yamutsi a wuraren kada kuri'a musamman saboda takun sakar da ke tsakanin jam'iyya me mulki da ta 'yan adawa Renamo wacce yarjejeniyar zaman lafiya ce da aka kulla a shekarar 1993 ta kai ta ga zama babbar jam'iyyar adawa wacce ko a shekarar 2012 jagoranta Afonso Dhlakama ya jagoranci wani karamin tawaye inda ya bayyana jam'iyyar Frelimo da nuna wa 'yan adawa banbanci a harkokin da suka shafi tattalin arziki.

Amma a cewar Judith Sargentini irin yadda suka ga yadda aka fito a tashoshin kada kuriar da alama za a kai ga gamawa lafiya.

"Daga irin tashoshin kada kuri'a da muka gani ,ina kara jaddawa wadanda muka gani, a lardina goma ya nuna cewa budewar lami lafiya kuma ko mai na tafiya"

Shi kuwa da ya ke nasa tsokacin shugaban hukumar zaben Abdul Carimo ya ce zabe ma na tafiya cikin nutsuwa se dai akwai wasu kananan matsaloli kamar bude wasu tashoshin kada kuri'a a makare da rashin isar wasu kayan aikin zaben kan lokaci da kuma batun gabatar da takardun shedar bada izinin sanya idanun yadda za a gudanar da zaben daga masu sanya idanu na waje.

Wahlen Mosambik 15.10.2014 Afonso Dhlakama
Dan takarar Renamo Afonso DhlakamaHoto: AFP/Getty Images/Gianluigi Guercia

Irin wannan matsalar ta cikar sharadun sanya idanun na daga cikin irin kalubale da masu sanya idanun na kungiyar EU suka bayyana cewa sun zame musu tarnaki kamar yadda Judith Sargentini ke cewa.

"A babban lardin jiha ba a bari masu sanya idanu ba daga Kungiyar Tarayyar Turai sun shiga tashoshin kada kuri'a ba bisa dalilan shugaban yankin cewa ba a buga hatimi ba kan takardun mu, nima ba a buga hatimi kan nawa amma wannan bashi ne batu ba"

Masu sanya idanu dai kan wannan zabe sun fito ne daga kasashen Kungiyar Tarayyar Turai da Kungiyar kasashen Kudancin Afrika da Kungiyar Tarayyar Afrika, a tsakiyar dare ne dai ake saran ganin inda alamun nasarar zaben ta karkataduk kuwa da cewa sakamako a hukumance zai bayyana ne nan da kwanaki goma sha biyar.