Kalubalen Birtaniya bayan fita daga EU | Labarai | DW | 04.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kalubalen Birtaniya bayan fita daga EU

Bayan da Birtaniya ta kada kuri'ar ficewa daga cikin kungiyar Tarayyar Turai, manyan jiga-jigan da suka jagoranci gangamin ficewarta na ci gaba da ajiye mukamansu.

Shugaban jam'iyyar UKIP ta Birtaniya Nigel Farage

Shugaban jam'iyyar UKIP ta Birtaniya Nigel Farage

Na baya-bayan nan shi ne Nigel Farage shugaban jam'iyyar United Kingdom Independence Party (UKIP) ta masu kishin kasa, wanda shi ma ya bayyana ajiye mukaminsa na shugabancin jam'iyyar. Da yake jawabi jim kadan bayan da ya ayyana ajiye mukamin nasa, Farage ya ce ba zai iya cimma wata nasara fiye da jagorantar kuri'ar raba gardamar domin ficewa daga kungiyar Trayarra Turan EU ba, a dangane da haka yake ganin ya kamata ya ajiye mukamin nasa na shugabanicin jami'iyaar ta UKIP. Ya kara da cewa:

"A gani na ya kamata mu samu Firaminista daga bangaren wadanda suka zabi ficewar daga Birtaniya. Mu samu mutumin da yake da jajircewa da kuma hangen nesa. Wannan shi ne babban abu a tarihin kasar nan. Kamar yadda na ke gani, kawo yanzu muna da 'yan takara uku wadanda suka marawa ficewar Birtaniya daga EU baya, ba kuma zan damu ba duk wanda ya samu nasarar lashe zabe a cikinsu zan mara masa baya a wannan lokaci."