Zaben tsakiyar wa'adi na Amirka
November 7, 2022Talla
Zaben wanda ake gani zai kasance zakaran gwajin dafi ga jam'iyyar Democrate ta Joe Biden na fuskantar babban kalubale daga jam'iyyar Republicain ta Donald Trump wanda ke da niyar sake tsayawa takara a zaben shugaban kasa na tafe. Mutane kamar miliyan 250 ake sa ran za su kada kuri'a domin zaben 'yan majalisar wakilai 435 a tsawon wa'adin mulkin shekaru biyu. A rana ta karshe ta yaki neman zabe Joe Biden ya jagorancin taron gangami a Jihar maryland da ke a gabashin Amirka kusa da Washington. Masu aiko da rahotanni na cewar yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine na iya yin tasiri a zaben.