Kalubale bayan shekaru 56 na ′yancin Kai a Nijar | Siyasa | DW | 03.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kalubale bayan shekaru 56 na 'yancin Kai a Nijar

Al'ummar Jamhuriyar Nijar sun gudanar da bukukuwan cika shekaru 56 da samun 'yancin Kai daga Faransa, a daidai lokacin da kasar ke fama tarin kalubale ciki har da na karancin abinci.

Shugaban Jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou

Shugaban Jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou

Jamhuriyar ta Nijar ta samu 'yancin cin gashin kan nata ne daga kasar Faransa a shekara ta 1960, hakan ne ya sanya kasar ke yin bukukuwan tunawa da ranar samun 'yancin kan a duk ranakun uku ga watan Agusta na ko wacce shekara.

A yayin wani jawabi da ya gabatar ga 'yan kasar Shugaba Issoufou Mahamadou na Jamhuriyar ta Nijar, ya tabo batutuwan tsaro da kuma ci-gaban da aka samu a fannin tattalin arziki da kyautata rayuwar jama'a. Sai dai tuni al'ummar kasar daga bangarori daban-daban ke bayyana ra'ayinsu dangane da jawabin da ma tunawa da wannan rana.

Jawabin shugaban na mintoci akalla 27 ya fi mayar da hankali ne a kan batun tsaro duba da halin yaki da ta'addancin da kasar take fama da shi, inda mayakan Boko Haram ke kai wa kasar farmaki a yankin Diffa.

Matsalar 'yan gudun hijira a Nijar sakamakon rikicin Boko Haram

Matsalar 'yan gudun hijira a Nijar sakamakon rikicin Boko Haram

Sai dai ya shafe dogon lokaci a jawabinsa yana bitar ayyukan c-gaban raya karkara da ya gudanar a wa'adin mulkinsa na farko tare kuma da karfafa cewar zai dora daga inda ya tsaya domin inganta rayuwar al'umma. Shugaba Mahamadou Issoufou ya kara da cewa:

Muhimman ayyuka a birane


"A tsawon shekaru biyar baya gaba dayan kasar nan ta ci moriyar muhimman ayyuka na makudan kudi ta hanyar gine-ginen da suka sauya fuskokin garuruwa kamar Yamai da Dosso da Maradi, baya ga wasu muhiiman ayyukan da muka kaddamar da soma aikinsu a wasu shekaru masu zuwa da suka hadar da madatsar ruwa da ake shirin kaddamarwa da sake karfafa matakan sauwaka tsarin sadarwa musamman ma na Internet."

Tallafin abinci ga al'umma sakamakon barazanar yunwa a wasu yankunan Nijar

Tallafin abinci ga al'umma sakamakon barazanar yunwa a wasu yankunan Nijar

Shugaban ya kuma tabo batun ilimi da fannin kiyon lafiya da yaki da karancin abinci, inda ya ce idan har an ce Nijar ta kaucewa fadawa a cikin yanayin karancin cimaka, to hakan ya faru ne ta hanyar tsarinsa na dan Nijar ya ciyar da dan Nijar da ake kira da "3N Day a Taimaka."

Martanin daga 'yan kasa da masana

Sai dai tuni masu sharhi a kasar ke ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan jawabin Malam Mamane Sani Adamou wani mai sharhi a Nijar din ya nunar da cewa:

"Duk wanda ya saurari kalaman shugaban kasa to lalle kam in dai a Nijar yake zai yi mamakin ko wannan kasar ce da muke ciki yake magana a kanta ko kuwa wata kasa can daban, domin wannan kasar da yake zance ba wadda muke raye a cikinta bace. Yau kusan shekaru hudu jere mu ne na baya, domin kasa ce wadda ci-gaban nata ba wai ba'ayin komai ba, a'a bai taka kara ya karya ba ne. Duk wata bukatarmu ta jin dadin rayuwa wannan bai taka kara ya karya ba. Kasar da ake bai wa tallafi na abinci ina ta ci da kanta?

Duba da tarin matsalolin da suka yi wa Jamhuriyar ta Nijar kawanya, dole ne hukumomin kasar da ke mulki a yanzu su yi wa matsalolin karatun ta natsu domin sake tafiya a cewar Alhaji Nouhou Mahamadou arzika na kungiyoyin MPCR .

Sauti da bidiyo akan labarin