Kalubalantar salon tafiyar da mulki a Nijer
July 10, 2013
Jam'iyyar MNSD Nassara mai adawa a jamhuriyar Nijer ta kira taron manema labarai a wannan Larabar (10.07.13) inda ta kalubalanci halin sakacin da gwamnatin jamhuriya ta bakwai take nunawa a fannoni da dama na tafiyar da mulkin kasa, kama daga mataki na tsaro zuwa almubazzaranci da dukiyar kasa, da ma rashin iya tafiyar da mulki.
Malam Ali Sabo, mataimakin shugaban jam'iyyar MNSD Nassara
reshen jihar Maradi shi ne ya jagoranci wannan taro, kuma ya tabo matsalolin da kasar ke fuskanta
"Akwai abubuwa da dama fiye da 100 da muke iya bayyana muku da suka yi da bai kamata ba, kuma ba mu zagesu ba, amma mun san rashin kulawarsu ce ta janyo wadannan matsaloli kuma muka ce a kula, sannan batun arzikin kasa kamar man fetur, kamar karfen Uranium duk kokowar da muka yi a baya tare da kamfanoni na waje sun byi watsi da su inda kowa ke kokarin cika aljihunsa maimakon yayi kokawa dan ci-gaban kasa domin shi kishin kasa abu ne mai wuya, dan haka kyawon da yayi kishin kasarsa."
Tsadar rayuwa da matsalar tsaro a Nijer
Da suke magana a fannin jin-dadin rayuwar al'umma , inda suka ce komai ya tsaya cik, rayuwa ta yi tsada sannan ga batun tsaro da ya kasance ana takura wa al'umma cikin kasa sannan da batun wasa da dukiyar kasa. Laouali Amadou, mai Zoumbou shi ne mataimakin shugaban jama'iyyar ta MNSD Nassara reshen jihar Dosso, yayi nashi tsokaci:
Yace "Wajan harkar tsaro magabatan na yanzu ba su dauki matakkan da ta kamata su dauka ba, kawai sai kada mutane na sanya tanonuwa a wurare, tare da sanya jami'an tsaro a gidajen su domin kariyarsu, abun da ya kamata, ita matsala tun kafin ta shigo ya kamata a ce an ganota kuma a dauki matakin maganceta musamman ma a fannin tsaro, mun gani lalle ayyukan da ake ana sanya kudade da dama a kansu. Misali, hanyar da za ta ci miliyan 15,000.00 sai ka ga anyi ta miliyan 30,000.00 a wannan gwamnati."
Tsawon awowi da dama ne 'yan adawar suka dauka suna baiwa 'yan jarida bayanai kan halin da kasar ta shiga na rashin tabbas a cewar su wanda kuma suka yi kira ga magabatan wannan kasa da su yi amfani da jan-hankalin da suke yi musu na gyara kayanka, amma ga bisa dukkan alamu a cewarsu, shiru ne har yanzu.
Martanin jam'iyyar PNDS dake mulki a Nijer
Sai dai daga nashi bangaren, mai kula da yada labarai na jama'iyyar PNDS Tarayya mai mulki, Malam Iro Sani, cewa yayi, wannan zargi nasu shaci-fadi ne, kuma suna yinshi ne dan kar a ce basu ce ba:
Yace "Wannan sanarwar tasu sanarwa ce ta wanda ba shi da wani abun fadi domin shaci-fadi ne kawai, ba dan sun fito sun fadi abun da suke so, ba zai zama gaskiya domin kowa na iya shiga cikin dakinsa ya sha fura ya fito ga fili yayi maganarsa yadda ya ga dama. Demokradiya haka ta gada amma gaskiyar lamarin shi ne kowa ya zo cikin wannan kasar ya san anyi aiki kuma aiki ne da yafi na tsawon shekaru goma da MNSD tayi tana mulki.
A halin yanzu dai, hankulan al'umma a wannan kasa ta jamhuriyar Nijer, sun karkata wajen jiran fitowar sabuwar gwamnati da ake rade- raden fiddowa wadda tun bata zoba ake jiran ta taka rawar gani sosai dan magance wasu matsalolin da ake ganin ta yanzun bata shawo kansu ba.
Mawallafi : Salissou Boukari
Edita : Saleh Umar Saleh