1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kafa sabuwar gwamnati a Tunusiya

Lateefa Mustapha Ja'afarAugust 29, 2016

A wannan Litinin din 29 ga wannan wata na Agusta da muke ciki, sabuwar gamnatin hadin kan kasa a Tunisiya za ta kama aiki.

https://p.dw.com/p/1JrX4
Sabon Firaministan Tunusiya Youssef Chahed
Sabon Firaministan Tunusiya Youssef ChahedHoto: Getty Images/AFP

Cikin sabuwar majalisar zartaswar sabuwar gwamnatin hadin kan kasar ta Tunisiya dai, har da mata da matasa. Da yake jawabi ga manema labarai gabanin kama aiki gadan-gadan, sabon Firaministan kasar Youssef Chahed ya sha alwashin jajircewa wajen kawo sauyi da sasauci a rayuwar kuncin da al'ummar kasar suka tsinci kansu a ciki, sakamakon rashin aikin yi da tabarbarewar tattalin arziki yana mai cewa:

"Gwamnatin hadin kan kasa ba za ta zamo gwamnati mai tsuke bakin aljihu ba, ko kuma rage ma'aikata. Za mu koma mu tsuke bakin aljihu ne kawai in mun rasa mafita."

Chahed da ke da shekaru 40 a duniya, na zaman Firaminista mafi karancin shekaru da aka taba yi a Tunisiya, tun bayan da kasar ta samu 'yancin kanta daga Faransa a shekara ta 1956, kana Firaminista na bakwai da aka yi a kasar cikin kasa da shekaru shida.