1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaduna: Matashiya mai sarrafa da 'ya'yan itace

April 20, 2022

Bayan kammala karatu a kwalejin horar da malamai ta kasa wata matashiya Aisha Adamu Ladan ta kirkiri kamfanin sayar da garin goroba da taura da magarya tare da sauran ‘ya’yan itace na gargajiya da ake yin shayi da su.

https://p.dw.com/p/4A8yl
Kastanie
Hoto: picture-alliance/dpa

Ita dai matashiyar Aisha Adamu Ladan ta ce wannan sana’ar ta sayar da 'ya'yan itatuwa ta zo mata a kan kari domin lokaci ya zo da al'umma da dama sun fara yin bankwana da tsoffin irin shayin da suke sha, sun fara komawa amfani da na gargajiya fiye da na sauran shayin zamani da ake kawo su daga kasashen ketare.

A cewarta dai akwai nasarori masu tarin yawa da ta samu, wadanda ke taimaka wa rayuwarta. Kalubalen da ta ce take fuskanta shi ne na rashin kayayyyakin sarrafa wadannan 'ya'yan itatuwa a zamance.

Bayan kammala karatu a kwalejin horar da malamai ta kasa, matashiyar ta kirkiri kamfanin sayar da garin goroba da taura da magarya tare da sauran ‘ya’yan itace na gargajiya da ake yin shayi da su.