Kaduna: Matashi mai sana′ar wanki da guga | Himma dai Matasa | DW | 03.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Kaduna: Matashi mai sana'ar wanki da guga

A Kaduna wani matashi mai karatun gaba da sakandire ya rungumi sana’ar wanki da guga gadan-gadan, ya kuma yi amfani da iliminsa wurin kawar da amfani da tsarin gargajiya zuwa na zamani.

Fotoreportage Hotel Chuabo in Quelimane Mosambik (Gerald Henzinger)

Wannan wani tsohon hoto ne muka yi amfani da shi na wani mai sana'ar wanki da guga na zamani

Matashin Felix Adams dan shekaru 39 da haihuwa dai kamar yadda ya bayar da misali ya ce aikin gwamnati ba ya iya samar da biyan bukatar rayuwa kamar yadda sana’ar hannu ke yi wa dan Adam. A saboda haka ne ma yake koyar da matasa wanki da guga don su dogara da kansu. Felix, Adams yana kokarin horas da matasan aiki nagari domin kalubalen sana'ar wanki da guga ya kan yi wa mutum kamari idan ya kasa faranta wa abokanan cinikayarsa rai. A yanzu haka dai Felix Adams ya yaye matasa guda goma da tuni suka bude shagunansu na wanki da guga a sassa daban-daban na garin Kaduna. Abin da ya sa ma ke'nan yake ganin bai dace matasa ‘yan boko su ci gaba da yin dogaro da gwamnati ba.

Sauti da bidiyo akan labarin