Kaddammar da watsa shirye-shirye zuwa na zamani a Najeriya | Siyasa | DW | 22.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kaddammar da watsa shirye-shirye zuwa na zamani a Najeriya

Najeriya da kadammar da tsarin watsa shirye-shirye zuwa na zamani a gidajen rediyo da talabijin na yankin Afirka ta Yamma kamar yadda hukumar sadarwa ta duniya ta sanya watan Yuni mai zuwa wa'adai.

Kaddamar da tsarin sauyin harkar yada labarai daga tsarin na da, da akan ce mai dungu zuwa na zamani da ke hade tashoshi a hanya guda, muhimmin mataki ne da gwamnatin Najeriyar ta dauka na kaiwa ga cimma wa'adin da hukumar sadarwa ta duniya ta tsara na watan Yunin 2017 ga kasashen Afirka.

Wannan aiki da ya dauki Najeriyar shekaru 12 ta na fafatawa kafin kaiwa ga matakin, na cike da alwashi na inganta yanayin aikin watsa shirye-shirye na radiyo da talabijin a kasar.

Somalia TV Fußball WM (picture alliance / dpa)

Ko da ya ke wannan muhimmin ci gaba ne na inganta yanayin aikin watsa labarai amma akwai tsoron haifar da rashin aikin yi saboda samun ci gaban kimiyya da fasaha da wasu ke nunawa. Najeriyar da ta fara harkar talabijin a 1959 a kasar dai, wadda a yanzu ta samu kaiwa ga wannan mataki a 2016, sau biyu ta na gaza cimma wa'adin da aka tsayar ga kasashen Afirka. An tsara cewa nan da watanni shida za'a fadada aikin zuwa shiyoyi shida na kasar domin cimma wa'adin.

Najeriyar dai na bukatar sabbin akwatunan talabijin da za su baiwa jama'a ikon kallon shirye shiryen talabijin ta wannan tsari har milyan 30 a kasar, domin wannan zai bai wa al'ummar kasar damar samun tashoshi na daukacin kasashen Afirka ta Yamma, abin da ya sanya tsara akwatunan bai daya ga kasashen yankin.

 

Sauti da bidiyo akan labarin