Kaddamar da bincike a kan kisan kimanin mutane 10 a Abuja | Siyasa | DW | 24.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kaddamar da bincike a kan kisan kimanin mutane 10 a Abuja

Majalisar dattawan Najeriya ta bi sahun kungiyoyin farar hula wajen binciken kisan wasu mutane kusa da rukunin gidajen 'yan majalisa da ke Apo.

Al'amura na kara lalacewa kuma fushi na al'umma na karuwa game da kisan wasu matasa kusan 10 da ake zargin jami'an tsaron cikin gida na SSS da yi a cikin makon jiya, da kuma ke ci gaba da tada hankali tsakanin sarki dama talakawan kasar ta Najeriya.

Na baya baya dai na zaman majalisar dattawan kasar da ta nuna bacin ranta bisa kisan, sannan kuma ta kafa wani kwamitin bincike da nufin tabbatar da gaskiyar abin da ya faru.

A wata muhawarar da ta dauki tsawon lokaci ana tafkawa dai, ra'ayi ya zo daya a tsakanin dattawan da suka ce tayi baki ta kuma baci ga batun cin zarafi na farar hula a sassa daban daban na kasar.

Senata Kabiru Ibrahim Gaya dai na zaman dan majalisar dattawan aaga Kano, kuma a cewar sa sun bai wa kwamitocin kare hakkin bil'adama da na Sharia'ar ta da su kaddamar da cikakken bincike a mika rahoto a cikin mako guda kacal.

Description en:House of Representatives of Nigeria Date 16 September 2005, 11:13 Source The House of Representatives Author Shiraz Chakera ou are free: to share – to copy, distribute and transmit the work to remix – to adapt the work Under the following conditions: attribution – You must attribute the work in the manner specified by the author or licensor (but not in any way that suggests that they endorse you or your use of the work). share alike – If you alter, transform, or build upon this work, you may distribute the resulting work only under the same or similar license to this one.

Ginin majalisar dokokin Najeriya

Makomar sakamakon binciken rigingimu a Najeriya

To, sai dai kuma kokarin bincike na gaskiya ko kuma kokarin kwantar da hankali dai, a baya majalisar ta kai ga kafa jerin kwamitoci a irin wannan matsala a Baga da Bama da Maiduguri da ma sassa daban daban na arewacin kasar, ba tare da yin wani tasiri ga kokarin sauya ko in kular jami'an tsaron tarayar Najeriyar ba.

Akwai ma dai tsoron yiwuwar cin shirwar mallam game da sakamakon binciken da ma kila matakan da 'yan kasar ke fatan gani cikin kasa da nufin adabo da izgilancin da ya sha sanadiyyar asarar rayuka a tituna da unguwanni na fararen hula.

To sai dai kuma a cewar Senata Sahabi Ya'u da tun da farko ya gabatar da bukatar binciken dai, babban aikin majalisar bai wuci mika wa bangaren zartarwar kasar sakamkon binciken domin cika nasu bangare na dokokin kasar.

To, sai dai ko ya zuwa yaushe ne dai al'ummar kasar ke shirin sanin gaskiyar abin da ya faru a unguwar ta Apo dai, tuni dai wata gaskiya mai daci a siyasar kasar ta fara baiyyana tare da shugaban tarayyar Najeriyar Goodluck Ebele Jonathan, ya shaida wa wani taro na 'yan kasar a birnin New York cewa fa lalle fa karen nan yana shirin sunsuna takalmin mulki a kasar.

Nigerian President Goodluck Jonathan waves as he arrives to attend the funeral service for writer Chinua Achebe at Ogidi in southeast Nigeria on May 23, 2013. Renowned author Professor Chinua Achebe was buried at his Ogidi country home. Hundreds of mourners gathered on Thursday in the hometown of Nigerian novelist Chinua Achebe for the funeral of the man regarded as the father of modern African literature and the author of the widely praised 'Things Fall Apart.' AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Yiwuwar takarar shugaba Jonathan a zaben 2015

Jonathan din da yanzu haka ke cikin tsakiyar wani rikicin cikin gidan da ke neman raba kan jam'iyyar sa ta PDP gida biyu dai, ya ce kundin tsarin mulkin kasar ya mika masa 'yancin mulki na shekaru takwas ba wai ba inke.

Abin kuma da ke zaman alamun ta lalace a cikin sulhun dake tsakanin 'ya'yan sabuwa da tsohuwar PDP amma kuma a fadar Barrister Abdullahi Jalo da ke zaman mataimakin kakakin PDP har yanzu da sauran fata.

Taba 'yanci ko kuma aiken sako dai, tuni masu adawa da takarar ta shugaban kasar suka fara karatun ganganci kuma wauta ga shugaban, na tuni wata takarar da ke iya daukar wa'adin mulkinsa zuwa shekaru sama da tara karkashin tsarin da a cewar Dakta Umar Ardo, wani masani na siyasa ya yarje masa shekaru takwas kacal.

Babban kalubale ga masu shari'ar dai na zaman ko shekara daya da kwanaki 23 na kama mulkin Jonathan na zaman cikin cikakken wa'adinsa ko kuma a'a.

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Saleh Umar Saleh

Sauti da bidiyo akan labarin