Kaci-kaci da DW ke yi | Amsoshin takardunku | DW | 09.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Kaci-kaci da DW ke yi

DW ta kwashe kimanin shekaru 30 tana gabatar da shirin kaci-kaci da masu sauraro ke samun kyautuka

Sashin Hausa na DW ya shafe shekaru kusan 30 yana shirya shirin gasar kaci-kaci, wanda ake yi domin bai wa masu sauraro kyautuka. Makasudin shirya gasar shi ne kara janyo hankalin mutane domin sauraron tashar, tare da bai wa masu sauraro damar samun kyautuka daban-daban.

Sashin kula da hulda da jama'a na tashar ke samar da kyautukan da ake rabawa, ko kuma wadanda suke ganin ya dace su bayar da taimako.

Babban dalilin da ya janyo ake kaci-kaci shi ne domin samun wata dama ta raba kyautukan. Aka gabatar da tambaya wadda ke cikin abubuwa da DW ke yada labarai a kai, domin kara wa masu sauraro kaimi.