Kace-nace tsakanin Rasha da Ukraine a kan harkar gas | Labarai | DW | 30.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kace-nace tsakanin Rasha da Ukraine a kan harkar gas

Shugaban Ukraine Viktor Yushchenko ya ba da umarnin daukar wasu jerin matakai don zaman cikin shirin ko-takwana dangane da tashin farashin iskar gas a cikin kasar. A cikin shagfinta na intanat, fadar shugaban kasar ta ce farashin gas da na wutar lantarki zai yi wani tashin gwauron zabi da ba´a taba gani ba a cikin kasar. Shugaba Yushchernko yayi kira ga hukumomin kasar da su kara yawan gas da suke samarwa a daidai lokacin da ake neman hanyoyin rage yawan amfani da gas. Hakan dai ya faru ne kwana guda kacal bayan an tashi baram-baram a tattaunawar da jami´an Ukraine da na Rasha ke yi da nufin warware wata takaddama da ta so sakamakon farashin gas. Rasha dai na son ta kara ninka farashin gas din da take sayarwa Ukraine har sau 4 don ya dace da farashin sa a kasuwannin duniya. Idan ba´a cimma wata yarjejeniya ba to Rasha ka iya dakatar da sayarwa Ukraine da gas a ranar lahadi mai zuwa.