1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashin da ya rungumi sana'ar burodi

Nasir Salisu Zango LMJ
October 17, 2018

Yayin da yawancin matasa da suka kammala karatun jami'a ke jiran samun aiki daga gwamnati, wani matashi mai suna Kabiru Hassan da ya kammala digirinsa ya shiga neman na kai.

https://p.dw.com/p/36j52

Shi dai matashi Kabiru Hassan ya nunar da cewa tun dab da zai kammala jami'arsa ya fara sana'ar rarraba burodin a shaguna kafin daga bisani ya koma ya koyi yadda ake gasa shi. Ya kara da cewa ya sha wahala matuka sai dai ya jajirce wajen ganin ya cimma burinsa. Bayan kammala koyon gasa burodin ne likkafarsa tai gaba, inda a yanzu ya bude masana'antar gasa burodin inda a yanzu yake da ma'aikata 20 kuma yana sake gina wani waje da yake ganin zai dauki matasa kimanin 30 aiki.

Kabiru Hassan mai biredi, ya bukaci matasa da su ajiye girman kai a gefe su yi kokarin koyon sana'o'in hannu, domin hakan ne kawai zai taimaka musu su zamo masu dogaro da kai ba sai sun jira aikin gwamnati ba. A cewar Kabiru koda ya samu aikin gwamnati ya san wata rana zai bari, hakan ce ma ta sanya ya rungumi sana'ar burodin domin ya zamo mai dogaro da kansa.