1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kabila ya nemi rigar kariyar bayan mulki

Abdul-raheem Hassan
June 16, 2018

Shugaban kasar Kwango Joseph Kabila ya bukaci dokar kare tsofaffin shugaban kasa a wani zaman majalisa na musamman kan wannan batu, lamarin da ake dangantawa da alama na sauka daga mulki.

https://p.dw.com/p/2zgHv
USA New York - Joseph Kabila Kabange in den UN Headquarters
Hoto: Getty Images/AFP/B. R. Smith

Majalisar dokokin kasar Kwango za ta yi wani zama na musamman domin duba bukatar shugaban kasar Joseph Kabila na samar da dokar da zai kare tsofaffin shugabanni kasar da suka bar mulki. Wannan mataki dai na dada nuna alamun yiwuwar shugaba kalbila zai iya sauka daga karagar mulki bayan babban zaben kasar a watan Disemba, duk da korafin da ake cewa shugaban na neman kara wa'adin shugabanci.

Babu dai tabbacin loakcin da majalisar za ta zauna don duba bukatar shugaban. Sai dai Kabila ya zarta wa'adinsa na mulki sakamakon rashin gudanar da zabe bisa dalilai na rashin kudi, lamarin da ya jefa Kwango cikin rikici na siyasa.