Köhler Muzambik | Siyasa | DW | 04.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Köhler Muzambik

Shugaban kasar Jamus ya isa Muzambik, zangonsa na farko a ziyararsa ga kasashen Afurka

Köhler a Muzambik

Köhler a Muzambik

Hanyoyin sadarwa a kasar ta Muzambik duk sun yi kaca-kaca lokacin da aka kawo karshen yakin basasanta misalin shekaru 16 da suka wuce. Amma kasar ta yi namijin kokari wajen daukar nagartattun matakai na garambawul a fannoni na siyasa da tattalin arziki, inda a yau ta wayi gari tana daya daga cikin kasashen Afurka dake samun bunkasar tattalin arziki a cikin hamzari. Kuma babban abin da ta sa gaba yanzu haka shi ne kara inganta manufofinta na ilimi da raya yankunan karkara in ji Jule Riviere, wacce ke da alhakin hada kan matakan taimakon raya kasa na Jamus a Maputo, fadar mulkin kasar ta Muzambik:

“A hakika kasar na fuskantar wata babbar kalubala saboda kaca-kaca da yakin basasanta yayi da makarantunta da kuma yaduwar kwayar HIV tsakanin malamai, sannan da yawa daga yara matasa ba su da ikon halartar ajujuwa.”

Amma duk da haka kasar Muzambik na kan wata nagartacciyar hanya kamar yadda shugaban kasar Jamus da tawagar dake masa rakiya a ziyarar tasa suka kara tabbatarwa. Shi kansa darektan ofishin cibiyar rancen sake ginawa ta Jamus a Maputo Carsten Sandhop ya lura da irin ci gaban da kasar Muzambik ke samu bisa manufa, amma kuma yayi bayani a game da wuraren da har yau ake bukatar karin hobbasa, inda yake cewar:

“Da farkon fari kasar ta kasance cikin mawuyacin hali sakamakon yakin basasanta da tabarbarar da dukkan tsare-tsare na rayuwa. A baya ga haka kasar ta kasance mai bin tafarkin gurguzu har ya zuwa karshen shekarun 1980. Amma kasar tayi namijin kokari wajen gabatar da matakanta na garambawul duk da matsalolin da ake fuskanta wajen sayar da kamfanonin gwamnati ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu da kuma tahakikanin gaskiyar cewa kasar ba ta da matsakaitan ‘yan kasuwa da zasu iya zuba jari a wadannan kamfanoni.”

Daya matsalar dake hana ruwa gudu kuma ita ce ta cin hanci da rashin wata dokar dake ba da kariya ga ‘yan kasuwa na ketare. Bugu da kari kuma Muzambik tayi shekaru kusan talatin tana karkashin wata jam’iyyar siyasa guda daya dake mulkinta kuma ‘yan hamayya ba su da wata rawa ta a zo a gani da suke takawa. Amma duk da haka kasar ta samu kyakkyawan ci gaba inda a cikin ‘yan shekaru kalilan ta kayyade yawan matalauta daga kashi 70 zuwa kashi 54%. Kazalika ta samu bunkasar yawan masu rajista a makarantun faramare sakamakon taimakon da take samu daga ketare. Jamus ta ware kudi Euro miliyan 67 domin tallafa mata a fannoni na ilimi da raya yankunanta na karkara tsakanin shekara ta 2005 da ta 2006.