Juyayin tuni da kisan kiyasu kan Yahudawa a Jamus zamanin mulkin Hitler | Zamantakewa | DW | 30.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Juyayin tuni da kisan kiyasu kan Yahudawa a Jamus zamanin mulkin Hitler

Duk da ƙoƙarin gwamnatin Jamus na yaƙi da aƙidar nazi masu ƙyamar Yahudawa na ƙaruwa a ƙasar

Symbolbild Israel Deutschland Jude

Kwana ta shi, an cika shekaru 80 daidai da Adolf Hitler ya zama shugaban gwamnatin Jamus.

A zamanin mulkin Nazi, Hitler ya ƙaddamar da wani shiri na aikata kisan kiyasu ga Yahudawa da aka fi sani da suna Holocaust.

A duk shekara idan ranar 30 ga watan Janairu ta zagayo, Majalisar Dokokin Bundestag na yin addu'o'i domin karrama dubun dubunan yahudawan da suka rasa rayuka zamanin mulkin Hitler.

Duk da ƙoƙarin gwamnatin tarayya Jamus na yaƙi da aiyukan Nazi har yanzu akwai Jamusawa da dama masu irin wannan alƙibla ta nuna kyama da wariya ga Yahudawa kamar yadda ita kanta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi baiyani:

"Babu shakka, mun tabbatar da ƙaruwa aiyukan 'yan nazi a Jamus, sabodan haɗin kan da wasu masu ilimi da wani kuma sashe na jama'a ke baiwa masu irin wannan mummunan aƙida.Saidai za mu cigaba da jajurcewa domin takaita yaɗuwar wannan aƙida" .

Zahlreiche Menschen nehmen am 27.01.2013 in Berlin an der Gedenkfeier für die Opfer des Nationalsozialismus teil. Während der Veranstaltung des Lesben- und Schwulenverbandes wurden am Denkmal für die im Nationalsozialismus verfolgten Homosexuellen im Tiergarten Kränze niedergelegt. Foto: Soeren Stache dpa

Tuni da yahudawan da suka rasa rayuka zamanin Hitler

A taraya Jamus akwai ƙungiyoyin Yahudawa masu yawa wanda suka ƙunshi membobi fiye da dubu 100.Mahimman aikin wannan ƙungiyoyi shine fafatukar kare kansu da kansu ga masu nuna masu wariya inji Daniel Alter wani limamin Yahudu a birnin Berlin, wanda kuma ya baiyana damuwa game da tsangwamar da ya ce suna fusknata:

"A gaskiya ba da kwanciyar hankali.Abin takaici aƙidar ƙyamar yahudawa ta zama tamkar ruwan dare a Jamus.Kusan kashi ɗaya cikin ukku na Jamusawa suna da wannan aƙida a baɗini ko zahiri".

Tun watan Nowemba shekara da ta gabata Daniel Alter ya zama memba a komitin da ke tantance tsangwamar da Yahudawa ke fama da ita anan Jmaus, ta hanyar tattatara kalamomin ɓatanci da cin mutunci da suke samu ta hanyoyin a sadarwa na zamanin, sannan ya miƙa su zuwa ga hukumomin shari'a.

Gwamnati Jamus ta dauki matakai,a duk wuraren ibada da haɗuwar bani yahudu da kuma makarantunsu.

Saidai banda jamusawa, suma matasa musulmi, larabawa ko 'yan asulin ƙasar Tukiyya su ka nuna ƙyama ga yahudawan Jamus.

Religious symbols, Paris, France, Europe

Cudayya tsakanin addinai

A wani mataki na neman cuɗe ni in cuɗe ka tsakanin mabiyya addinai daban-daban Ahmed Mansur wani ɗan Palestinu dake birnin Berlin ya ƙaddamar da wani shiri na faɗakarwa:

" A gaskiya kyamar Yahudawa na kara bazuwa, saboda haka ya zuama wajibi a saami fahintar juna a fadakar da jama'a kan mahimmancin zama tare."

A cikin laccocin da ya ke gabatarawa, Ahmed Mansur na faɗakar da jama'a domin su daina ɗaukar dukan yahudawa tamkar maƙiya musulmi sannan su kuma yahudawansu daina ɗaukar dukan musulmi a matsayin masu adawa da yahudanci.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu