1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Myke tyson zai sake komawa damben boxing

Mouhamadou Awal Balarabe AH
July 27, 2020

Juventus ta Turin ta zama zakaran da Allah ya nufa da cara a karo na tara a jere cikin tarihin kwallon kafa ta Serie A na Italiya wannan da ma wasu na daga cikin abubuwan da suka dauki hankali a Labarin Wasanni.

https://p.dw.com/p/3fxrn
Italien Serie A | Fußball-Meisterschaft von Juventus Turin
Juventus ta ItaliyaHoto: AFP/M. Bertorello

Makonni biyu kafin karshen kakar kwallon kafa a Italiya, Juventus ta yi nasarar yi wa takwarorinta zarrar maki bakwai mai wuyar cikewa bayan da ta doke Sampdoria da ci 2-0, lamarin da ya ba ta damar sake zama zakarar kasar a karo na tara a jere. Godiya ta tabbata ga Christiano Ronaldo da Frederici Bernadesci da suka zura kwallayen biyu a ragar abokan karawa a mako na 36 na gasar Seria A ta Italiya. Wannan bajintar ta gwarzo ta bai wa Juventus Turin damar kafa tarihin lashe Scudetto wato kambun zakara na Italiya so 36 cikin tarihinta. Hasali ma wannan matsayin shi ne na farko da kungiyar ta samu a karkashin horaswar Maurizio Sarri, wanda ya fara aiki a bazarar shekarar da ta gabata, ma'ana yana neman bin kafar kochi Antonio Conte wanda Juventus ta zama zakarar sau uku karkashin umurninsa da kuma Massimiliano Allegri da ci Turin ta zama gwana sau biyar.

Wasannin Premier Lig bayan gudanar da wasannin mako na 38 a karshen mako

Fußball Premier League Chelsea wird englischer Meister | Ballack und Lampard
 Premier Lig Chelsea Hoto: picture-alliance/dpa/G. Penny

A Ingila, an yi ban kwana da kakar kwallon kafa ta Premier Lig bayan gudanar da wasannin mako na 38 a karshen mako. Wannan ya ba da damar sanin raguwar kungiyoyi da za su wakilci kasar a gasakannin Turai. Dama dai Liverpool da Manchester City sun riga sun samu tikitinsu na gasar zakarun Turai dai, amma Manchester United da Chelsea sun cike raguwar guraben biyu da aka saba ware wa Ingila, bayan da suka samu matsayi na uku da na hudu a teburin Premier Lig saboda kowaccensu ta doke abokiyar karawa Leicester da Wolverhampthon da ci 2-0. yanzu ta Champions. A bangaren Europe Lig kuwa, Leicester da Tottenham za su wakilci wannan kasa. Wannan yana nufin cewar kungiyar Arsenal da ita ma ke fada ana ji a Premier Lig ba ta kai bantenta a cancantar shiga gasannin Turai ba, amma tana da sauran dama daya da ta rage mata na lashe kofin kwallon kafar Ingila da za ta buga da Chelsea a karshen mako. Sai dai tuni aka san dan wasan da ya zama gwani na gwanaye a bana a Premier lig, wanda ba wani ba ne illa Keftain na kungiyar Liverpool Jordan Henderson, bayan da doke  Kevin de Bruyne, Marcus Rashford da Virgil Van Dijk da Sadio a kurin'un da marubuta labarin wasanni suka kada. Sai dai Jordan Henderson ya ce ya samu wannan bajinta ne sakamakon goyan baya da ya sa samu daga abokan wasanshi.

Mike Tyson na shirin komawa na shirin sake komawa fagen dabem boxing

Mike Tyson
Mike TysonHoto: Imago Images/D. Rosenblum

A Amirka, tsohon zakaran damben boxing nan Mike Tyson na shirin komawa fagen dagga don nuna cewa har yanzu yana da suran kwarjini kare kansa duk da cewa shekarunsa sun fara turawa. Cikin wani sako da ya wallafa a shafin yanar gizonsa ne, Tyson ya sanar da cewa zai fafata da Roy Jones, mai shekaru 51, a ranar 12 ga Satumba a Los Angeles. Babu dai wasu bayyanai game da yanayin da za a yi wanna damben, sai dai ana ganin wasa ne na kawa na ran sarki ya dade. Ayar tambaya a nan ita ce mai ya sa tsohon taurarin damben duniya ajin mai masu nauyi yake nemi warware tubar da ya yi daga damben bayan kusan shekaru 16 da kwance damarsa ?  Shi dai Mike Tyson ya yi damben boxing tsakanin shekarun 1980 zuwa' 90s ya samu nasarar a manyan dambe 50 da ya yi, lamarin da ya sa  ba za a iya mantawa da shi ba tsakanin manyan 'yan damben duniya ba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani