Julius Nyerere: Gagarabadan Shugaba a Afirka | Tushen Afirka: mutanen da suka taka rawa a tarihin Afirka | DW | 15.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Tushen Afirka

Julius Nyerere: Gagarabadan Shugaba a Afirka

Nyerere wanda fitaccen dan kishin kasa ne ya taimaka wajen ganin Tanganyika ta samu mulkin kai, inda daga bisani ta hade da Zanzibar a matsayin kasa guda da ake kira Tanzaniya.

Rayuwarsa: 

An haife shi a shekarar 1922 a garin Butiama na Tanganyika, wadda daga baya ta zama kasar Tanzaniya. Ya yi karatunsa a jami'ar Makerere ta kasar Yuganda, inda ya fito a matsayin kwararren malamin makaranta. Daga bisani ya karanci tattalin arziki da tarihi a jami'ar Edinburgh. Ya rasu a London a shekarar 1999.

 

Abubuwan da ya yi fice a kai:

·  Lakabinsa na "Mwalimu" wanda yake nufin malami a harshen Swahili. Nyerere ya koyar da ilimin hallitu da Turancin Ingilishi shekaru uku kafin ya jagoranci nema wa Tanganyika mulkin kai, inda daga bisani ya zama shugaban kasar, wadda aka sauyawa suna zuwa Tanzaniya bayan hade Tanganyika da Zanzibar.

·  Irin yadda yake kaunar ganin nahiyar Afirka ta kasance tsintsiya madaurinki daya, sai dai sabanin da ke akwai tsakaninsa da Kwame Nkrumah ya sanya shi kafa kungiyar kasashen gabashin Afirka a matsayin matakin farko yayin da Nkrumah ke neman a girka kungiyar kasashen Afirka. Daga bisani shugannin biyu ne suka share fagen kafa kungiyar tarayyar Afirka ta AU.

·  Karbar sojin sa kai na Afirka: Bayan samun 'yancin kai da kasarsa ta yi, Nyerere ya bi tafarkinsa na kishin nahiyar Afirka ta hanyar tallafawa sojin sa kai da suka yi wa gwamnatocin Mozambik da Afirka ta Kudu da Namibiya tawaye.

·  Fassara littatafan William Shakespeare zuwa harshen Swahili.

A dubi bidiyo 01:31

Julius Nyerere: Jagoran samun 'yanci

Cimma burinsa: 

A lokacin da ake yakin cacar baka, Nyerere bai hada kansa da kowa ba. A lokacin da Jamus ta bukaci kasarsa da ta raba gari da tsarin nan na hulda da kasashen ketare na Hallstein Doctrine ya ki amincewa da haka duk kuwa da hadarin da zai iya fuskanta na rasa kudaden tallafi daga Jamus din. A wannan lokacin ya nace kan cewar kasarsa 'yantacciyar kasa ce don haka ba wanda zai sanya ta yin abin da ba ta yi niyya ba.

 

Abubuwan da suka jawo masa suka:  

Kin amincewa da ra'ayoyin da suka sha bamban da nasa da kuma yin watsi da mayakan sa kai da aka yi gwagwarmaya tare na daga cikin abubuwan da suka sanya aka rika sukar Nyerere. An kuma ce yana adawa da irin karfin fada a jin da malaman addini ke da shi a Tanzaniya. Wani abu da aka soke shi a kai shi ne shirin nan nasa na Ujmaa wanda bai yi nasara wajen kawo sauyi ga tattalin arzikin Tanzaniya ba. Sakamakon haka ne ya yi murabus a shekarar 1985 don ba da dama ta yin sauye-sauye na tattalin arziki.

Ujamaa: 

Matsayinsa na wanda ya fito daga gidan yawa, ya yi kokarin amfani da tsarin na hadaka da yin aiki tare da nufin cimma abin da aka sanya a gaba. Ujamaa wanda aka samo daga harshen Swahili na nufin iyali. Ya yi hulda da Jomo Kenyatta na kasar Kenya kuma a wani lokaci ma ya yi tunanin a ba wa Kenyatta dama ta shugabantar yankin gabashin Afirka baki daya. A kan haka ne ma ya yi yunkurin jinkirta nema wa Tanganyika mulkin kai har sai sauran kasashen uku sun samu, duka dai da fatan hade kan kasashen waje guda. Sai dai sauran shugabannin kasashen ba su bashi goyon baya ba amma kuma hakan bai sanyaya masa gwiwa ba. Ya mai da hankalinsa wajen hade kabilun Tanzaniya waje guda ta hanyar amfani da Swahili a matsayin harshen da za a rika yin magana da shi a hukumance.

 

Kalamansa da suka shahara:

"Uhuru na kazi ('yanci da aiki)"

"Ba wata kasa da take da 'yanci na yankewa wata abin da za ta yi."

"Hadewa waje guda ba zai sa mu yi arziki ba amma hakan zai sa a daina cin zarafi da tozarta mutanen Afirka da kasashensu."

"Ilimi ba hanya ba ce ta kaucewa shiga talauci, hanya ce ta fafutuka."

"In har ana son samun ci gaba na kirki to dole ne a dama da al'umma."

 

Shiri na musamman "Tushen Afirka" aiki ne na hadin gwiwa tsakanin DW da Gidauniyar Gerda Henkel.

Sauti da bidiyo akan labarin