1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

JTF ta ce ta kashe 'yan bindiga a Kano

March 31, 2013

Rundunar tsaro ta JTF reshen kano ta yi wani artabu da wasu mayaka da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne inda ta hallaka 14 daga cikinsu, yayin da soja daya ya mutu.

https://p.dw.com/p/187VT
Hoto: Getty Images/AFP

Rundunar tsaro ta hadin guywa a jihar kano wato JTF ta bayyana cewa ta yi nasarar harbe wasu 'yan bindiga 14 yayin wata arangama  da safiyar wannan lahadin.Karar harbin bindigogi da fashewar bama bamai sun yi ta tashi a yankin unguwa uku da kanon.

Kakakin rundunar na jihar kano Keptain Ikedechi Iweaha ya bayyana cewar dakarun sun yi artabu da wasu mutane da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram. Ya kuma tabbatar da cewar soja guda ya rasa ransa yayin da wani guda kuma ya sami mummunan rauni . Keptain Iweaha ya kuma nunar da cewa dakarun rundunar sun hallaka 'yan bindiga 14 bayan tarin makamai da bama bamai da suka samu a wasu  gidajen.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mouhamadou Auwal Balarabe