Josina Machel - Mai fafutukar kare hakkin mata a Mozambik | Tushen Afirka: mutanen da suka taka rawa a tarihin Afirka | DW | 15.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Tushen Afirka

Josina Machel - Mai fafutukar kare hakkin mata a Mozambik

Josina Machel ta yi kokari a fafutukar kare hakkin mata karkashin Turawan mulkin mallaka. Sai dai ta mutu tana da shekaru 25 ba tare da ganin cikar burinta na samun 'yanci a kan idonta ba.

Wace ce Josina Machel?

An haifi Josina Abiathar Muthemba a ranar 10 ga watan Agusta na shekara ta 1945 a lardin Inhambane da ke a kudancin Mozambik. Sabanin mata 'yan Afirka a wancan lokaci, iyayenta sun ba ta karfin gwiwa ta je makaranta. A shekara ta 1956 ta koma babban birnin kasar da a lokacin ake kira Lourenco Marques, inda ta shiga makarantar sakandaren koyon fasaha.

A can ne Machel ta shiga harkokin siyasa na kungiyoyin dalibai gadan-gadan, inda ta zama mamba ta kungiyar masu fafutukar neman 'yanci ta Mozambique Liberation Front, wacce Turawan Portugal suka fi sani da FRELIMO a takaice. Jam'iyyar siyasa da ta fi fice a Mozambik a yanzu haka. An kafa FRELIMO a shekara ta 1962 a Tanzaniya don fafutukar neman 'yancin Mozambik daga mulkin Portugal.

 

Ta yaya Josina Machel ta ba da gudunmawa a fafutukar samun 'yanci? 

A lokacin tana da shekaru 18 a duniya, Josina Machel ta yi hijira zuwa Mozambik da niyar shiga yakin kwatar 'yanci daga Turawan Portugal. A yunkurinta na farko an kamata a Southern Rhodesia, wacce ake kira a yau da sunan (Zimbabuwe). An mayar da ita gida, inda aka tsareta a kurkuku na tsawon watanni. A yunkuri na biyu ne sai da ta dangana shalkwatar FRELIMO a babban birnin Dar es Salaam na Tanzaniya. Kimanin tafiyar kilomita 3,500.

Ta samu horon soja har ta kai cikakkiyar 'yar FRELIMO. Ta jagoranci harkokin kula da jama'a a jam'iyyar a shekarar 1969 a lokacin tana da shekaru 24. A shekarar ta auri Samora Moises Machel, wanda ya ci gaba da fafutuka har ta kai shi ga zama shugaban kasar Mozambik na farko. Sai dai Josina ba ta rayu ta ga kasar Mozambik a matsayin kasa mai cin gashin kanta ba, kasar da ta samu 'yanci a shekarar ta 1975. Bayan fama da rashin lafiya mai tsanani ta rasu a birnin Dar es Salaam a shekarar 1971.

 

A dubi bidiyo 01:57

Josina Machel - Mai fafutukar kare hakkin mata a Mozambik

Me ya sa Josina Machel yin fice?

Saboda tsayawurta tsayin daka a fafutukar samun 'yanci, ta ki karbar tallafin karatu zuwa Switzerland, inda ta gwammace ta zauna a gida ta ci gaba da fafutuka cikin sojojin sa kai masu adawa da Portugal. Ta kuma yi yaki kan hakkokin mata, domin a basu dama su shiga a fafata da su a fafutukar neman 'yanci, kama daga daukar makamai har zuwa fafutuka a siyasance.


Ita kadai ce mace 'yar fafutukar neman 'yancin?

Tabbas akwai wasu matan da suka shiga fafutuka har suka sanya kaki. Da yawa sun samu karfin gwiwa ne saboda ganin irin nasarar da Josina ta cimma. Dalilan da suka sa Josina Machel ta yi fice sun hadar da sadaukar da kai da mutuwar da ta yi da wuri da auren mutumin da daga bisani ya zama shugaban kasar Mozambik, wadannan na daga cikin dalilan da suka sanya ake tunawa da ita.

 

Wane abin koyi ta bari?

Josina Machel ana tunawa da ita a duk lokacin da ranar mutuwarta ta zagayo, wato bakwai ga watan Afrilu. A kasar Mozambik wannan ranar mata ce ta kasa da ake tuna fafutukarta ta ganin an daidaita hakki tsakanin maza da mata.

 

Glória Sousa da Leonel Matias da Gwendolin Hilse sun yi hidima wajen hada labarin da ke zama na musamman "Tushen Afirka" mai zuwa kashi-kashi  da DW ke gabatarwa da hadin gwiwar cibiyar Gerda Henkel.

Sauti da bidiyo akan labarin