Jose Mujika shugaban ƙasar da ya fi talauci a duniya | Amsoshin takardunku | DW | 17.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Jose Mujika shugaban ƙasar da ya fi talauci a duniya

Wane dalilai su ka sa a ke dangata shugaban ƙasar Yurugai Jose Mujika a matsayin shugaban da ya fi talauci?

epa03404633 Uruguayan President, Jose Mujica, speaks during the welcome ceremony for the Jose Leonardo Chirinos, which belongs to the Venezolana de Navegacion Corporation (Venavega), the first Venezuelan ship arriving to a Mercosur economic organization port, in Montevideo, Uruguay, 20 September 2012. The ship arrived from Puerto Cabello, Venezuela, transporting 14,000 tons of urea for the production of fertilizers for Uruguayan agriculture and 55,000 liters of agrochemicals. EPA/IVAN FRANCO +++(c) dpa - Bildfunk+++

Jose Mujika

An haifi Jose Mujika ranar 20 ga watan Mayu na shekara 1935 wato yanzu ya na da shekaru 77 kenan a duniya, an haife shi Montevideo babban birnin ƙasar Yurugai.Kuma iyayensa talakawa ne ƙwarai, asulinsu 'yan ci rani ne daga ƙasar Italiya su ka zo suka zamna a Yurugai.

Tun ya na ɗan saurayi ya shiga rundunar tawayen Tupamaros wadda ta yi gwagwarmaya da dakarun gwamnatin Yurugai.

A cikin wannan fada ne sojoji gwamnati suka caflke shi a matsayin firsina sai da ya share shekaru 14 tsare a kurkuku daga 1973 zuwa 1985.Daga cikin shekarun 14 na zama gidan kurkuku, yayi shekaru biyu tsare cikin rijiya saidai a zura mashi abinci.

An sako shi daga kurkuku a shekara 1985 bayan da ƙasar Yurugai ta rungumi tsarin mulkin demokraɗiyya.

Bayan an sako shi daga gidan yari tare da wasu abokan gwagwarmaya sai su ka girka jam'iyar siyasa da suka radawa suna MLN-T, domin ƙwatar mulki ta hanyar demokraɗiyya, wato kenan su ajje makamai.

Leaders attend the Mercosur summit in Montevideo, Uruguay,Tuesday, Dec. 20, 2011. South America's Mercosur trade bloc approved a Palestinian free trade deal Tuesday and then pushed to admit Venezuela as a full member, even at the cost of threatening its founding principles. (Foto:Matilde Campodonico/AP/dapd)

Taron kungiyar Mercosur a Montevideo babban birnin Yurugai

A ƙarƙashin wannan jam'iya ne aka zaɓi shi dan Majalisa,sannan kuma ya Senata, kamin daga bisani a naɗa shi ministan noma da raya ƙasa.A shiga zaɓen shugaban ƙasa a shekara 2009, inda ya samu nasara tare da kashi 53 na ƙuri'un da aka kaɗa.

An rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasar Yurugai ranar ɗaya ga watan Maris na shekara 2010.

Mi yasa aka cewa shine shugaban ƙasar da ya fi ko wane talauci a duniya?

Na farko tun lokacin da aka rantsar da shi ya ce albashinsa shugaban ƙasa da yake samu kimanin Euro 10.000 ko wane wata, zai ware kashi 90 cikin dari ga ƙungiyoyin bada agaji ko kuma ga mabuƙata, wato daga cikin wannan kuɗaɗe Euro 10.000 zai ɗauki Eurto 1000 kaɗai sun wadace shi.

Sannan gidan da yake ciki a yanzu haka, irin gidan nan ne na gona.A Turai har ma ƙasashen Afirka manoma kan aza 'yan bukkoki cikin gonarsu, saboda rage yawan kai da koma ,daga gida zuwa gona, to shugaban Yurugai Mujika a cikin irin wannan gida ya ke, kuma gidan ma ba na shi ne ba, na matarasa ne mai suna Lucia Topolansky.A gidan saɓanin ƙasashemu inda gidan shugaban ƙasa ke jibge da sojoji shaƙe da bindigogi, a gidan shugaban Yurugai 'yan sanda biyu ne rak ke gadi.

Kullum safiya dake gidan ba cikin gari ya ke sai a tuko shi cikin tsohuwar motarsa azuwa wurin aiki da yamma kuma a tuka shi a maida shi gida ba tare da jiniya ba kokuma wata tawagar soja.

Idan ma dai ba kan san motarsa ba,idan da ya wuce ba za ka iya gane shugaban ƙasa ne ba.Sannan abun mamaki har yanzu ba bar noma ba , aikin da ya saba yi da matarsa kamin a zaɓe shi shugaban ƙasa.

** ALTERNATIVE CROP OF EDB152 ** Uruguay's president-elect Jose Mujica, left, gestures to supporters in Montevideo, Sunday, Nov. 29, 2009. Mujica, a former leftist rebel, won just over 50 percent of the votes according to exit polls by all three of the country's leading pollsters.(AP Photo/Natacha Pisarenko)

Jose Mujika

Kafofin sadarwa da dama sun yi ta zuwa a gidansa suna fira da shi, suna tambayarsa mi yasa ya ke rayuwa haka cikin talauci, alhali ga shi ya samu matsayin shugaban ƙasa.Amsar da yake ba su kullum iri guda ce:Ya na ce masu ni ba matalauci ba ne,ba na bukatar facaka ne a rayuwata, ya na basu misali da babban ma'aikacin Yurugai bai wuce albashin Euro 900 awata, kuma ya ishesa yin rayuwarsa,saboda haka bai ga dalilin da zai sa shi ya ɗauki albashi fiye da haka.

Ya na ce basu shi a tunaninsa rayuwa abu uku ne zuwa huɗu wato soyyaya, mutum ya so dan uwansa,sannan iyali, da kuma amminai.

Shi kuɗi a gare shi ba abun damuwa ne ba saboda idan ya tara su na duniya zai barinsu saboda haka a maimakon ya yi ta tara kudi ya fi dacewa ya ɗauki abinda ke isar shi sannan sauran ya taimakawa mabuƙata.

Sannan ya na ce masu a tsawan rayuwarasa ya share shekaru 14 kulle a kurkuku, daga cikin shekaru biyu yayi cikin rijiya, kuma kamin ma a kama shi kurkuku yayi fiye da shekaru goma bai da katifa, saidai ya shimfiɗa tabarma ƙasa ya kwanta.Saboda kimamin Euro dubu da ya ke samu ko wane wata sun ishe shi yayi rayuwarsa cikin rufin asiri.

To ka ji kaɗan daga dalilai da suka sa ake cewa shugaban Yurugai Jose Mujika shine ya fi ko wane talauci a duniya.

A cikin irin wannan yanayi ta ƙaƙa Mujika zai iya aiyukan ƙasa, mussamman hulɗoɗi da ƙasashe ƙetare?

Babu wata matsala, yadda ka san ko wane shugaba ya na gudanar da mulki shima haka.Kuma a lokacinsa, al'umar Yurugai sun ga cenci sosai ta fannin cigaban ƙasa saboda an samu ragowa ta fannin cin hanci da rashawa, saboda kyakkyawan misalin da shugaban ke badawa.

Veranstaltung mit dem Staatspräsidenten von Uruguay José Mujica. 18.10.2011, Friedrich Ebert Stiftung. copyright: DW/Eva Usi

Jose Mujika a Jamus bisa gayyatar Gidauniyar Friedrich Ebert Stiftung

Sannan a yanzu tarmamuwar Yurgai nan haskakawa kwarai a yankin kasashenLatine Amurika,da kuma a Majalisar Dinkin Duniya domin ƙasar ta na bada gudummuwa sosai a aiyukan Majalisar.

A zamanin mulkinsa Mujika, Yurugai ce ƙasa ta biyu a yankin Latine Amurika bayan Brazil ta fannin bada tallafi mai yawa a Majalisar Dinkin Duniya.

A taƙaice dai kafofin sadarwa sun nunar da cewa lalle duk ɗan Adam ajizi ne, ba zai rasa kura-kurai ba, amma haƙiƙa ɗabi' o' in shugaban Yurugai na yanzu abin koyi ga shuganin ba ma na Afrika har ma na sauran ƙasashen duniya.

Mawallafi: Yahouza Sadisou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal