1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Jordan za ta yi taro na musamman kan agazawa Falasdinawa

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 11, 2024

Taron zai mayar da hankali wajen kiran kasashen duniya da kungiyoyin agaji domin tallafawa Falasdinawan Gaza da ke fama da rashin abinci da ruwa da wutar lantarki

https://p.dw.com/p/4gtOr
Hoto: Habboub Ramez/abaca/picture alliance

Jordan za ta ka karbi bakuncin taro na musamman a Talatar nan kan hanzarta kai agajin jin-kai ga Falasdinawa, bayan Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin fadawar yankin cikin matsanacin halin yunwa, sanadiyyar shafe sama da watanni 8 ana yakin Gaza.

Karin bayani:Amirka na neman MDD ta kada kuri'a kan yakin Gaza

Taron dai na hadin gwiwa ne da Majalisar Dinkin Duniya da kuma Masar, kuma zai samu halartar jagoran Falasdinawa Mahmoud Abbas, tare da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, a ziyararsa ta 8 yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan barkewar rikicin.

Karin bayani:Isra'ila ta halaka Falasdinawa 200 kafin ta kubutar da hudu

Ana sa ran taron zai mayar da hankali wajen kiran kasashen duniya da kungiyoyin agaji domin tallafawa Falasdinawan Gaza da ke fama da rashin abinci da ruwa da wutar lantarki.