Jonathan ya ziyarci wadanda hari ya rutsa da su. | Labarai | DW | 27.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jonathan ya ziyarci wadanda hari ya rutsa da su.

Shugaban Najeriya ya kai ziyara a asibitin Abuja, domin gane wa idanunsa wadanda suka jikkata sakamakon harin da aka kai a Emab Plaza dake babban birnin tarayya.

Shugaban dai ya katse halartar babban zaman taron kungiyar tarayyar Afirka dake gudana a birnin Malabo, sakamakon harin da aka kai a wata cibiyar kasuwanci dake Abuja. Jonathan ya ziyarci wadanda suka jikkata sakamakon harin, dake kwankwance a asibiti, bayan da ya fara da ziyartar Emab Plaza dake tsakiyar birnin na Abuja, inda harin na bam din ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21.

A wani takitaccen bayani da yayi a gaban manema labarai, Shugaba Goodluck Jonathan ya ce Najeriya ta shiga cikin wani yanayi mafi muni, wanda masu muguwar akida suka jefat. Ya kara da cewar 'yan Najeriya na kokawar ganin kasarsu ta bunkasa, kuma suna aiki tukuru domin su yi tattali iyallansu, yayin da wasu daga wani bangare ke da burin kashe mutane kawai.

Wannan hari ya kasance na uku a cikin watanni uku da Abuja ya fuskanta, lamarin da ke haifar da shakkun a zukatan al'umma dangane da kasawar hukumomin na samar da tsaro dangane da tashin hankalin da 'yan Boko Haram ke haddasawa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe