John Kerry zai tattauna da shugabannin Isra′ila da Falasɗinu | Labarai | DW | 31.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

John Kerry zai tattauna da shugabannin Isra'ila da Falasɗinu

Sakataran harkokin wajen Amirka John Kerry ya fara yin wata ziyara aiki a Yankin Gabas ta Tsakiya

Kerry wanda ya isa a yau birnin Tel-Aviv, an shirya zai gana da firaminsta Isra'ila Benjamin Netanyahu a birnin Ƙudus, da kuma jagoran falasɗinawa Mahamud Abbas a Ramallah, kafin ya isa a Brussel a gobe Talata idan zai halarci taron Ƙungiyar NATO.

Isra'ila dai ta ƙi ta saki wani rukunin na ƙarshe na fursunan Falasɗinu a ranar Asabar da ta gabata kamar yadda aka tsara a tattaunawar ta farfaɗo da zaman lafiya a yanki Gabas ta Tsakiyar. Tana mai cewar za ta sake sune kawai, idan Falasɗinu ta amince a ƙara tsawaita wa'adin tattaunwar ta gaba da gaba da nufin samun zaman lafiya wadda wa'adinta ke kawo ƙarshe a ranar 29 ga watan Afrilu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal