John Kerry ya kai wata ziyarar ba zata a Bagadaza | Labarai | DW | 10.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

John Kerry ya kai wata ziyarar ba zata a Bagadaza

Wannan ziyarar da ba a sanar tun farko ba, tana cikin rangadin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da yake yi da nufin hada karfi don yakar kungiyar IS.

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya kai ziyara Bagadaza babban birnin kasar Iraki don tattaunawa da shugabannin kasar. Ba a dai sanar da kai wannan ziyara ba da ke cikin rangadin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da Kerry din ke yi da nufin samun goyon bayan shugabannin yankin a yakin da ake yi da mayakan kungiyar IS mai da'awar kafa daular Musulunci a Iraki da Siriya. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amirka ya ce Kerry zai gana da sabon Firaministan Iraki Haidar al-Abadi da shugaban kasa Fuad Massum da ministan harkokin waje Ibrahim Jafari sai kuma shugaban majalisar dokoki Salim al-Jaburi. Wannan ziyara a Bagadaza ta zo ne sa'o'i kalilan gabanin wani jawabi da Shugaba Barack Obama zai yi wa al'ummar Amirka inda zai gabatar da manufofin yakinsa da kungiyar IS.