1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Joe Biden yayi alwashin hada kan 'yan kasar

Abdoulaye Mamane Amadou
November 8, 2020

Zababben shugaban Amirka Joe Biden yayi alwashin hada kan 'yan kasar jim kadan bayan tabbatar da nasararsa a zaben shugabancin kasar da aka shafe tsawon kwanaki ana dakon sakamako.

https://p.dw.com/p/3l17V
USA Wilmington | Rede Joe Biden und Kamala Harris nach dem Wahlsieg
Hoto: Jim Watsion/AFP/Getty Images

A yayin jawabinsa ga 'yan kasar daga Delaware, Biden ya ce baya bukatar rarraba kan 'yan kasar fatansa shi ne na hada kansu kana lokaci yayi a yanzu da takamata a warkar da Amirka.

Tuni dai zababben shugaban ya ambaci kafa wani sabon kwamiti kwararru da za su yi cikakken nazari kan hanyoyyin magance annobar corona da ta yi mumunan illa wa kasar tun daga gobe Litinin, kana su gabatar da wasu shawararwarin da za a soma aiki da tu tun daga ranar 20 ga watan Janairun shekarar badi ranr da zai fara kama aiki.

A yanzu hakan daga ko ina cikin kasashen duniya ana ci gaba da taya Mista Joe Biden murnan samun nasara ciki har da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, wanda ya bayyana Biden a matsayin babban abokin Isra'ila.