Joe Biden ya tattauna da shugabannin Iraƙi | Labarai | DW | 19.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Joe Biden ya tattauna da shugabannin Iraƙi

Mataimakin shugaban Amirka Joe Biden ya buƙaci shugabannin Iraƙin da su haɗa kansu ta hanyar kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa.

Joe Biden ya tattauna ta wayar tarho da shugabannin Iraƙin guda uku dangane da farmaki da masu kishin addini 'yan Sunni suka ƙaddamar a ƙasar. Biden ya tattauna daban-daban da firaminista Nuri al Maliki ,sannan kuma da tsohon shugaban majalisar dokokin da aka rusa ɗan Sunni Usama al Nudjaifi da kuma shugaban yankin ƙurdawa Massud Barzani.

A lokacin tattaunwar ya ce a kwai buƙatar a samu haɗin kansu domin tinkarar tashin hankalin da ƙasar ta samu kanta a cikinsa, ta hanyar kafa gwamnatin haɗaka wacce ya ce yakamata ta yi aiki da sakamakon zaɓe na bayabaya nan da aka gudanar. Wannan tattaunawa na zuwa ne a dai ai lokaci da Iraƙin ta buƙaci taimakon Amirka a hukumance domin fuskantar 'yan tawayen na ISIS da ke barazanar ƙwace yankunan ƙasar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu