Joe Biden ya samu tikitin kalubalantar Trump | Labarai | DW | 19.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Joe Biden ya samu tikitin kalubalantar Trump

Babban taron jam'iyyar adawar Amirka ta Democrat ya yi ittifakin cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Joe Biden zai dawo da Amirka kan turba madaidaiciya idan har ya samu damar kayar da Shugaba Donald Trump.

Jiga-jigan jam'iyyar sun yi wannan ikirari ne a ranar Talata da daddare lokacin bikin tabbatar da Joe Biden a matsayin dan takarar Democrat a hukumance. Uwargidan dan takarar na Democract Jill Biden ta sha alwashin cewa mijinta ba zai ba Amirkawa kunya ba.

Joe Biden ya kasance mataimakin shugaban kasa a karkashin gwamnatin tsohon Shugaba Barack Obama daga shekara ta 2009 zuwa 2017, ya kuma samu tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar ta Democrat a bana ne bayan ya yi rashin nasarar samu a shekarun 1988 da kuma 2008.