Joe Biden ya ki tsayawa takara a Amirka | Labarai | DW | 21.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Joe Biden ya ki tsayawa takara a Amirka

Biden bai fito fili ya bayyana goyon bayansa ga kowanne dan takara a jam'iyyar Democrats ba, amma kuma rashin tsayawarsa takara ya bude wa Clinton kofa.

Mataimakin shugaban kasar Amirka Joe Biden ya bayyana cewa ba zai tsaya takarar shugabancin kasar ba a zaben Amirkan da ke tafe a shekara ta 2016 mai zuwa. Bayyana matsayar tasa da Beiden ya yi ya kawo karshen dakon da aka yi na tsahon watannin na tunanin tsayawarsa takara da kuma kawo karshen al'amuran siyasarsa da ya kwashe shekaru masu tarin yawa yana yi.

Matakin kin tsayawar Bidan takara ya bude kofa ga matar tsohon shugaban kasar ta Amirka wato Hillary Rodham Clinton wadda ke neman jam'iyyarsu ta Democrats ta tsayar da ita a matsayin 'yar takara a zaben na badi.

Ko da yake Beiden bai fito fili ya bayyana goyon bayansa ga kowanne dan takara a jam'iyyar tasu ba, amma ya ce ya na fatan duk wanda jam'iyyar ta Democrats ta tsayar zai dora a kan inda Shugaba Barack Obama da ke kammala wa'adin mulkinsa ya tsaya.