Jodan za ta ci gaba da yaƙi da IS | Labarai | DW | 05.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jodan za ta ci gaba da yaƙi da IS

Wannan kisa a ƙone mutum a cikin keji ya tada hankulan al'ummar ƙasar ta Jordan dama na sauran ƙasashen duniya, inda ita ƙasar ta Jordan ta bayyana aniyar zafafa yaƙin da take yi da IS.

Jordanien König Abdullah II 04.02.2015

Sarki Abdallah na Jodan

Sarki Abdallah na ƙasar Jodan ya bayyana cewar akwai babbban martani da za a maida wa Ƙungiyar IS bayan kisan matuƙin jirgin yakin ƙasar Jodan, kamar yadda kafar yaɗa labaran ƙasar ta bayyana.

Sarki Abdallah ya ce za su shiga yaki da mayakan ka'in da na in bayan kisan wasu mayaƙan sakai guda biyu.

Wannan martani dai na zuwa ne bayan da mayakan na IS suka bayyana hoton bidiyo na IS lokacin da suke kona Muath al-Kasasbeh.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Abdurrahman Hassane