Jirgin sojan Amirka ya fadi a Afghanistan | Labarai | DW | 02.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin sojan Amirka ya fadi a Afghanistan

Jirgin sanfarin C-130 mai kula da jigilar sojoji, ya fado da kimanin shabiyun daran Alhamis wayewar Jumma'a kusa da filin jirgin saman birnin Jalalabad.

Wata sanarwa ta rundunar sojan kasa ta kasar Amirka ta bakin Kanal Brian Tribus, ta ce dukannin mutane11 da ke cikin jirgin sun rasu, cikinsu sojojin Amirka shidda. Sai dai kuma a wata sanarwa da ta fitar ta shafinta na Tiwtta kungiyar Taliban ta hanyar kakakinta Zabihullah Mujahid, ta dauki alhakin kai wannan hari tare da kakkabo jirgin na Amirka.

Kawo yanzu dai babu wani bayani daga bengaran kungiyar NATO kan wannan lamari. Sojojin na Amirka dai na aiki ne karkashin kungiyar tsaro ta NATO a wani mataki na bayar da tallafin horo ga sojojin kasar Afghanistan. Jirgin dai an tsarashi ne ta yadda zai iya tashi ko sauka a gajeriyar hanya ko kuma wani dan fili da akayi wa kwaskwarima, sannan kuma yana da injimi har guda hudu.