1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsuntsaye sun sa jirgi saukar gaggawa

Binta Aliyu Zurmi
August 15, 2019

An jinjinawa wani matukin jirgin saman fasinja na kasar Rasha bayan da ya yi saukar gaggawa lokacin da wasu tsuntsaya masu yawa suka shiga cikin injin jirgin.

https://p.dw.com/p/3Ny1F
Russland nahe Ramenskoye | Airbus A321 der Ural Airline Notlandung im Feld
Hoto: Imago Images/ITAR-TASS/Russian Emergency Situations Ministry

Jirgin dai ya sauka lafiya a wata gona ba tare da an rasa rai ko daya ba sai dai mutum guda ya jikkata yayin da wasu da dama suka nemi ganin likita bayan da aka kwashesu daga cikin jirgin.

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasar ta ce irin yadda ma'aikatan jirgin suka tinkari lamarin abin a jinjina musu ne. Jirgin kirar A321 da ke dauke da fasinjoji 226 da ma'aikata 7 ya tashi ne daga filin jirgin sama na Moscow zuwa Simferopol da ke Crimea.