Jirgin sama ya kama da wuta a Rasha | Labarai | DW | 05.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin sama ya kama da wuta a Rasha

Mutane 13 sun mutu wasu 10 sun jikkata bayan da jirgin sama dauke da fasinjoji 73 ya yi saukar gaggawa a filin sauka da tashin jirage a birnin Moscow bayan da jirgin ya kama da wuta jim kadan bayan tashinsa.

Matukin jirgin ya karkata akalar jirgin cikin gaggawa zuwa filin saukar jirage da ke Moscow bayan da wani fasinja ya sanar da ma'aikatan jirgin ya ga wuta na ci a wani bangare na jirgin.

Kafofin watsa labaran kasar Rasha sun wallafa hotunan yadda wuta ya kama jirgin tare da tirnikewar hayaki,  sai dai babu karin bayani a hukumance nan take kan musabbabin da ya sa jirgin ya kama da wuta, amma hukumomin kula da sufurin jiragen sama na kasar Rasha na ci gaba da binciken lamarin bayan da jirgin ya yi saukar ba shiri ba tsammani. Ana kuma kula da wadan da suka jikkata.