Jirgin sama ya bace a gabashin Indonisiya | Labarai | DW | 31.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin sama ya bace a gabashin Indonisiya

Hukumomin kula sufirin jiragen sama a Lardin Papua da ke gabashin Indonisiya, sun bayyana batan dabon jirgin saman dakon kaya dauke da mutane hudu. Jami'ai sun ce jirgin ya tura sakon gaggawa kamin a daina samun bayanai.

Jami'ai da ke kula zirga-zirgan jirage a kasar sun ce an dena jin duriyar jirgin ne bayan sa'a guda da tashinsa a loakcin da ya shiga tsakanin wasu tsaunuka da ke gabashin kasar. Jirgin sanfurin PK-SWW ya tashi ne daga garin Timika da misalin karfe 10:57 a daren Lahadi tare da fasinjoji biyu da matuka jirgin biyu, jirgin na dauke da kaya.

Masu aiyukan ceto a kasar dai sun ce suna ci gaba nemo karin bayanai a kan dalilan bacewar jirgin dama inda ya ke a halin yanzu, to sai dai kawo yanzu rashin kyawun yanayi na kawo teko ga aiyukan gudanar da binciken yadda ya dace. Wannan dai ba shi ne karon farko da jiragen sama ke batan dabo a yankin ba ganin harkokin sufiri ya ta'allaka ne ga jiragen sama saboda rashin kyan tituna da tsaunuka da suka mamaye yankin.