1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin sama a Kano

Abba BashirOctober 11, 2006

Shekarar da jirgin sama ya fara zuwa Kano

https://p.dw.com/p/BvVC
Jiragen Sama
Jiragen SamaHoto: AP

Jamaa masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na wasikun ma su sauraro,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fitone daga hannun Malama Yalwa Isma’il “Yar Jihar Kano, amma mazauniya a Jidda, Makkatul-Mukarramah. Malamar cewa ta yi; A wace shekara Jirgin sama ya fara zuwa Kano, kuma a Yaushe ne aka bude filin Jirgin-sama na Malam Aminu Kano?

Amsa: Jirgin-sama ya fara zuwa Kano, a tsakanin shekarun 1924 zuwa 1925, wato kimanin shekaru 81 zuwa 82 kenan da suka wuce. Hakan dai ya faru ne a zamanin Sarkin kano Shehu, inda a wancan lokaci a wata Unguwa da ake kira Bamfai da ke Birnin na kano, Jirage guda biyu masu saukar Ungulu suka fara sauka a wannan Fili na Bamfai.

Bayan saukar wadannan Jirage sai turawan Mulkin-Mallaka na wancan lokaci, suka gayyaci Sarkin Kano Shehu da Hakiman sa, domin su je su ga irin wadannan Jirage, inda suka amsa wannan gayyata, kuma harma suka shiga cikin Jirgin aka dana su. Daga baya sai aka sake sabon filin Jirgin sama kusa da dai inda wancan na da din yake, a dai dai wurin da ake kira Tukurwa, wanda a yanzu za’a iya cewa Katsina Road.Kuma an gina wannan sabon Filin-jirgi a shekarar 1933, lokacin Sarkin Kano Abdullahi Bayero, yana da wajen Shekaru 7 a kan karagar Mulki.

Bayan “yan shekaru, sai aka dan dada matsawa kadan, inda ka gina sabon Babban Filin-jirgin sama da ake kira, (Kano International Airport) wanda aka bude a shekarar1954. Kuma Ministan Sadarwa na Najeriya a wancan lokaci, wato Chief K.O.Imbadiwe, shine ya jagoranci bikin budeshi. An gina shine a kan kudi, Fan din Ingila Dubu dari-biyar. A yanzu wannan Babban Filin-jirgin sama, shi ake yi wa lakabi da Malam Aminu Kano International Airport.