1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin ruwan Libiya ya shiɗe lodin kayan taimakon Gaza a Misira

July 15, 2010

Gidauniyar agaji ta Ƙaddafi Foundation ta kasa cimma nasarar sauke lodi a tashar jiragen ruwan Gaza.

https://p.dw.com/p/OJWB
Jirgin ruwan Libiya ɗauke da kayan agaji zuwa GazaHoto: AP

Bayan kwanaki da dama na ta ci ba ta ci ba, a ƙarshe dai jirgin ruwan nan da ƙasar Libiya ta lodoma tan dubu biyu na kayan agaji zuwa Gaza, zai shiɗe lodin a tashar jiragen ruwan Masar.

Da farko Gidauniyar bada agaji ta Ƙaddafi Foundation da ta samar da kayan, ta yi kunnen uwar shegu ga kashedin da hukumomin Isra´ila suka yi, na cewar kar ta kuskura ta shiɗe lodin a tashar jiragen ruwan Gaza. Kakakin gwamnatin Isra´ila Chamselassil Ayari ya bayyana hujjojin haramcin da cewa tun da farko sun sanar da Libiya kar ma ta jarraba sauke lodin wannan kaya a tashar jiragen ruwan Gaza, domin sai ta ratsa ta gaɓar ruwansu alhali babu wata ma´amila da Libiya ta fannin zirga-zirgar cikin ruwa. Isra´ila ta ce su shiɗe lodin a tashar jiragen ruwan Misira, kuma ta yi alƙawarin za ta jigilar wannan kaya zuwa ga al´ummar gaza.

Wannan taƙƙadama dai, ta zo makwanni shidda, bayan da dakarun Isra´ila suka kai hari ga wasu jiragen ruwan Turkiyya ɗauke da kayan agaji zuwa Gaza, inda mutane tara suka rasa rayukansu.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Mohammad Nasiru Awal