Jirgin ruwa ya kife da bakin haure | Labarai | DW | 30.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin ruwa ya kife da bakin haure

Kimanin bakin haure 30 aka ceto sannan 84 suka bace sakamakon lumewar da jirgin ya yi a cikin tekun da ke tsakanin Libiya da kasashen Turai.

Jami'an tsaron ruwan Italiya sun bayyana cewar kimanin 'yan gudun hijira 26 aka ceto sakamakon nitsewar da jirgin su ya yi tekun bahar Rum da ke tsakanin Libiya da Turai a yayin da 84 har yanzu aka kasa gano inda suke a tekun ba.

Jami'an tsaron ruwan Italiyan sun ce sun sami wani kiran wayar tafi da gidanka wacce ta taimaka musu lalubo inda bakin hauren suke, a inda suka sami nasasar ceto 26 daga cikin kwalekwalen daya nitse a kusa da garin Sabratha.

Har ya zuwa yanzu dai babu wasu bayanai da ke nuni da cewar ga daga indabakin hauren suka fito ko kuma kasashensu. Ana ci gaba da gudanar da bincike a dangane da lamarin.

Fiye dai da mutane dubu dari 300 ke kauracewa talauci da yake-yake a nahiyar Afirka kan yi amfani da mashigar Libiya domin kai wa zuwa ga nahiyar Turai.