Jiragen saman Isra´ila sun sake kai hari cikin dare kan ´yan Hamas | Labarai | DW | 20.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jiragen saman Isra´ila sun sake kai hari cikin dare kan ´yan Hamas

Majiyoyin asibiti sun ce wani hari ta sama da Isra´ila ta kai cikin dare a kan wata mota a Zirin Gaza ya halaka mutane 3. Wani kakakin sojin Isra´ila ya tabbatar da cewa wani hari da suka kai ya afkawa wata motar ´yan takifen Hamas. A jiya asabar Isra´ila ta kashe Falasdinawa 4 a wani farmaki da ta kai ta sama. Rundunar sojin Isra´ila ta ce jiragen saman ta na ci gaba da kai hari a Gaza don hana magoya bayan Hamas harba rokoki zuwa kudancin Isra´ila. A kuma halin da ake ciki kungiyoyin Falasdinawa da ba sa ga maciji da juna sun fara wani sabon yunkuri na tsagaita wuta, irinsa na biyar a cikin mako guda da aka kwashe ana dauki ba dadi wanda ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 51.