1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jiragen ruwan Chaina da Philippine sun yi karo da juna

August 19, 2024

Jiragen ruwa na kasashen Chaina da Philippine suka yi taho mu gama a lokacin wata arangama a kusa da wani ruwa da ake takaddama a kai a tekun kudancin Chaina.

https://p.dw.com/p/4jboV
Masu tuka jiragen ruwan Philippine
Masu tuka jiragen ruwan PhilippineHoto: ARMED FORCES OF THE PHILIPPINES/AFP

Gwamnatin Beijing ta zargi jiragen ruwan Philippine da yin karo da jiragenta da gangan. Masu gadin gabar ruwan China sun ce sun dauki matakin da ya dace kamar yadda doka ta tanadar. A nata martanin, gwamnatin Philippine ta ce, jiragen ruwanta biyu sun lalace, kamar yadda ita ma ta dora alhakin karon ga kasar Chaina, ta na mai bayyana shi a matsayin wuce gona da iri da Chainar ke yi.

Karin bayani: Sabon takun saka ya barke tsakanin China da Philippines

Kasashen Kudu maso Gabashin Asiya da dama sun yi ikrarin cin karo da juna a tekun kudancin Chaina, da Chaina ta ke ikrarin iko da kusan dukanninshi.