1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jiragen ruwa sun fitar da abinci daga Ukraine

November 1, 2022

Bayan sanarwar da Rasha ta yi game da janyewa daga yarjejeniyar fitar da kayan abinci daga Ukraine, bayanai sun tabbatar da fitar jirage da kayan abinci ta teku.

https://p.dw.com/p/4IvzJ
Istanbul Getreidefrachter aus Ukraine warten auf Durchfahrt durch Bosporus
Hoto: Khalil Hamra/AP/picture alliance

Akalla jiragen ruwa na dakon kaya uku ne aka tabbatar da cewa sun bar gabar ruwan Ukraine a wannan Talatar shake da hatsi, duk da sanarwar janyewar da Rasha ta yi daga yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya kan fitar abinci da aka yi a Turkiyya.

Kamar dai yadda wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar, rukunin jiragen na ruwa na kan hanyar zuwa kasashen Jamus da Libiya da kuma Moroko dauke da sama da tan dubu 84 na hatsin.

Kusan dai tan miliyan 10 ne na kayan abinci suka fita daga Ukraine, tun bayan fara aiki da yarjejeniyar da aka sanya wa hannu cikin watan Yuli, kafin barazanar da Rasha ta yi game da batun a karshen makon jiya.

Tun ranar Lahadin da ta gabata ce Majalisar Dinkin Duniya da Turkiyya da ma kasar Ukraine suka amince da ci gaba da jigilar kayan abincin, duk da cewa ba su samu tabbacin Rasha za ta bayar da damar wucewa ba.