Jiragen kasa biyu sunyi karo a faransa | Labarai | DW | 11.10.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jiragen kasa biyu sunyi karo a faransa

Mutane 12 ne suka rasa rayukansu kana wasu da dama suka jikkata ,alokacinda wani jirgin kasa na pasinja yayi karo da wani na daukan kaya a yankin arewa maso gabashin kasar faransa.Jirgin pasinjan na tafiya ne daga Luxembourg zuwa birnin Nancy,lokacinda ya hadu da hadarin ayau a garin Zoufftgen,wanda ke cikin kasar faransa akan iyaka.Kakakin hukumar jiragen kasa ta kasar faransa ,ya danganta hadarin jiragen biyu da gyaran hanyoyin jiragen kasa da ake gudanarwa,wanda yasa jirgin pasinjan yabar ainihin hanyarsa,inda yayi karo dana daukan kayan.

 • Kwanan wata 11.10.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu5B
 • Kwanan wata 11.10.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu5B