1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirage sun cigaba da tashi a nahiyar Turai

April 21, 2010

An cigaba da harkokin sufurin jiragen sama a nahiyar turai

https://p.dw.com/p/N2Qq
Hoto: AP

Filayen jiragen saman na nahiyar turai sun cigaba da harkokin su na zirga zirga a ranar larabar nan inda fasinjoji ke ta karakaina domin samun jirgin da za su mayar da su gida. Hukumar kula da sufurin jiragen sama a nahiyar turai tace ana sa ran tashin kashi uku bisa hudu na jirage a ɗaukacin ƙasashen na nahiyar turai. Tsaikon zirga zirgar sufurin da gajimaren tokar ta haifar dai ya janyowa kamfanonin jiragen saman hasarar fiye da Dala Biliyan 1.7 kamar yadda daraktan hukumar Giovanni Bisignani ya baiyana.

"Yace girman wannan lamarin yayi munin da zaá iya cewa ya fi na lokacin harin nan na 11 ga watan Satumba 2001".

Yace aƙalla zai ɗauki hukumomin jiragen saman shekaru uku kafin su farfaɗo daga hasarar da suka tabka. A saboda haka ya buƙaci gwamnatoci su duba yiwuwar hanyoyin da zasu taimakawa kamfanonin jiragen domin rage musu raɗaɗin hasarar da suka yi.

Shima da yake tsokaci shugaban kamfanin jiragen sama na Lufthansa Wolfgang Mayrhuber yace a nasu ɓangaren ba zasu aike da buƙatar tallafi ba.    

" Yace ba zamu nemi wani tallafi ba, za dai mu duba yadda zamu iya tunkarar alámura da kan mu".

Wolfgang Mayrhuber yace idan zaá ƙididdiga hasarar da kamfanin na Lufthansa yayi ta doshi kimanin euro miliyan 200. Yace to amma suna fatan mayar da wannan hasara nan mako mai zuwa idan alámura suka inganta.

A halin da ake ciki hannun jarin kamfanin na Lufthansa ya tashi da kimanin kashi ɗaya da ɗigo ɗaya a kasuwannin hada hadar hannun jari. Shi ma kamfanin Britsh Airways hannun jarinsa ya tashi da kashi ɗaya da ɗigo biyu yayin da kamfanin KLM nasa hannun jarin ya tashi da ɗigo tara.

An dai ɗage tarnaki akan zirga zirgar sufurin jiragen sama na dogon zango a yawancin ƙasashen turan da suka haɗa da Jamus da Birtaniya.

Ana sa ran jigilar jirage 21,000 a wannan rana ta laraba. Shugaban kamfanin Britsh Airways Willie Walsh yace soki lamirin taƙaita zirga zirgar jiragen wanda yace bai dace ba hasali ma yace ya ƙara jefa jamaá cikin halin ƙunci.

Shima kamfanin Emirate yace yana fatan cigaba da jigilar kwasar fasinjoji inda ya buƙaci fasinjojin da su ƙara haƙuri.                      

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala   

Edita : Umaru Aliyu