1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikice

An dage zaman sukhun Habasha

Suleiman Babayo MAB
October 7, 2022

Majiyoyin diflomasiyya sun tabbatar da jinkirta zaman sulhu kawo karshen rikici tsakanin mayakan yankin Tigray da gwamnatin Habasha karkashin kungiyar Tarayyar Afirka da aka tsara a Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/4Hu2w
Luftangriff trifft Mekelle, Region Tigray
Hoto: Tigrai TV/REUTERS

An jinkirta zaman tattaunawa tsakanin gwamnatin Habasha da mayakan yankin Tigray karkashin kungiyar Tarayyar Afirka da aka tsara a karshen mako. Kamfanin dillancin labaran Associated Press na AP, ya ruwaito cewa majiyoyin diplomasiyya sun tabbatar da jinkirta zaman sulhun domin kawo karshen rikicin na shekaru biyu.

Ranar Laraba da ta gabata gwamnatin Habasha ta tabbatar da amsa gayyatar zuwa zaman sulhu a kasar Afirka ta Kudu, karkashin kungiyar Tarayyar Afirka.

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo zai jagoranci zaman sasanta bangarorin na yankin Tigray da gwamnatin Habasha, tare da tallafin Uhuru Kenyatta tsohon shugban Kenya, gami da Phumzile Mlambo-Ngcuka tsohuwar mataimakiyar shugabar kasra Afirka ta Kudu.

A watan Nuwamba na shekara ta 2020 rikici ya barke tsakanin gwamnatin Habasha da mayakan yankin Tigray abin da ya raba milyoyin mutane daga gidajensu.