Jinkiri kan sake rijistan masu zabe a Ghana | Siyasa | DW | 21.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jinkiri kan sake rijistan masu zabe a Ghana

A wani mataki na neman shayo kan wannan matsala kan sake rijistan masu zaben, cibiyar matsin lambar gwamnati akan al’amuran tattalin arziki (IEA), ta shirya wani taro don samun mafita.

Ita dai babbar jam’iyya mai mulki a kasar ta Ghana NDC, ta bijirewa taron ne tare da jingina hujjarta a kan cewa IEA na yunkurin baiwa kanta ikon da ba nata ba, domin kuwa hukumar zaben kasar ne kadai ya cancanta ta dau wannan matakin. Kofi Adams shi ne mai hada kan jama’a na jam’iyyar na kasa baki daya, ya bayyana hujjarsu na kauracewa taron.

"Wannan tamkar bata lokaci ne. Ai bayan hukuncin kotun koli akan shari’ar kalubalantar ingancin zabukan shekarar 2012, ita IEA din nan ta tafka muhawara da dama da dukannin jam’iyyun siyasa har ma da wadanda basu da wakilci a majalisar dokoki, inda ta sa muka rattaba yarjejeniyoyi da dama, wadanda kuma aka gabatar wa hukumar zaben a matsayin shawarwarin da hadin gwiwar jam’iyyun suka tsaida, ita ma ta tsananta bincike har sau biyu akansu kana ta bai wa kowane bangare damar gabatar da matsayinsa akan rajistar kamin ranar 22 ga watan da ya gabata na Salumba. A dalilin haka wannan matakin daga IEA ya zo a makare, saboda hukumar zabe ta kammala nazarorinta har ma ta saka ranekun 29 da 30 na wannan wata na Oktoba domin tattaunawa akan shawararin da aka gabatar mata."

Sai dai a nata bangaren cibiyar ta IEA ta yi Allah wadai da matsayin jam’iyyar NDC inda ta ce wannan wani abin kunya ne, domin kuwa wannan muhawara an yi ta ne domin amfanin kasa, ba wai domin wani bangare ba. Kawo yanzu dai kusoshin jam’iyyun siyasa dama tsaffin jami’an gwamnati ne suka saka baki a cikin kiranyen, ciki har da tsohon mataimakin kakakin majalisar dokoki Farfesa Mike Ockway, wanda ya nuna ra’ayin cewar, ba tilas ba ne a sake rajisata a ko wace shekara…

"Akwai bukatar hukumar zabe ta gudanar da cikaken bincike a game da dukannin zarge-zargen da suka mamaye ingancin rajistan zaben, kuma tayi amfani da ikon ta wajen daidaita al’amura a cikin hanzari domin kare zaman lafiya da ci gaban kasar."

Sauti da bidiyo akan labarin