Jikin Nelson Mandela ya kara yin tsanani | Labarai | DW | 24.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jikin Nelson Mandela ya kara yin tsanani

Rahotanni daga Afirka ta Kudu na cewa jikin tsohon shugaban kasar Nelson Mandela ya kara yin tsanani a tsukin sa'o'i ashirin da hudun da suka gabata.

FILE - This photo taken July 18, 2012 shows former South African President Nelson Mandela during the celebration of his 94th birthday in Qunu, South Africa. Mandela’s condition remained serious but stable on Monday, 10.6.2013, his third day in a Pretoria hospital, the South African government said. (AP Photo/Schalk van Zuydam, File) pixel

Südafrika Nelson Mandela Archivbild 18.07.2012

A ranar Lahadi ce dai fadar gwamnatin Afirka ta Kudun ta bada wannan labarin inda kakakin gwamnatin kasar Mac Mahraj ya ce shugaba Jacob Zuma ya bukaci al'ummar kasar da su sanya Mandela cikin addu'o'insu daidai lokacin da Mr. Zuma ya zayarci dattijon a asibiti, inda ya kara da cewar likitoci na ta bakin kokarinsu wajen ganin ya samu lafiya.

Tuni dai iyalansa musamman ma dai 'ya'yansa da kuma tsohuwar mai dakinsa Winnie Mandela suka je asibitin domin kasancewa da tsohon dan gwagwarmaya da wariyar launin fatar dan shekaru casa'in da hudu da haihuwa, yayin da al'ummar kasar ke ci gaba da nuna alhinunsu dangane da halin da Mandelan ke ciki.

A kwanaki sha bakwai din da suka gabata ne dai aka sake kwantar da Mandela bayan da cutar huhun da yake fama da ita ta ta'azzara.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal